A yau, Asabar, an gudanar da babban bikin baje kolin al’adun gargajiya a masarautar Kaltungo, a Jihar Gombe, inda dubban mutane suka halarta daga cikin jihar da wajenta.
A yayin taron, an yi raye-raye da nuna al’adun gargajiya, ciki har da irin abincin gargajiya da aka gada tun kaka-da-kanni a masarautar Kaltungo da sauran masarautun maƙwabta.
- Hukumar Ilimin Bai Daya Za Ta Gina Dakunan Karatun Zamani A Makarantun Nijeriya
- Gwamnatin Tarayya Ta Rabar Da Naira Biliyan 16.1 Ga Masana’antu 22 — Ministan Kudi
Taron na bana ya gudana a filin wasanni na tunawa da Obasanjo da ke Kaltungo, inda manyan baki da sarakunan gargajiya daga yankunan Arewa suka halarta.
Haka kuma, tsohon ministan yaɗa labarai, Farfesa Jerry Gana, ya gabatar da jawabi, yayin da Mr. Meso C. Dickson ya kasance babban baƙon taron.
Mai martaba Sarkin Kaltungo, Injiniya Sale Muhammadu Umar, ya gode wa sarakunan gargajiya bisa amsa gayyatarsa.
Ya bayyana cewa ana shirya wannan taron domin tallafa wa cigaban al’adu, da kuma karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin mazauna masarautar da makwabtanta.
Ga hotunan bikin: