Gwamnatin Jihar Kano ta ba da gudummawar motocin sintiri 78 ga Rundunar ‘Yansandan Jihar, don inganta ayyukan tsaro.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya mika motocin a wajen bikin da aka yi a Fadar Gwamnatin jihar, inda ya yaba wa ‘yansanda kan kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya tare da alkawarin ci gaba da goyon baya.
- Binciken Ra’ayoyi na CGTN: Masu Ba Da Amsa Na Sa Ran Ganin Kasar Sin Ta Karfafa Hadin Gwiwar Asiya Da Pacific
- Bankin Duniya Da IMF Na Kassara Tsarin Ilimin Jami’o’i A Nijeriya – ASUU
“Wadannan motocin za su inganta tsaro da kuma samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci,” in ji Gwamna Yusuf, bayan ya jaddada jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaro.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Salman Dogo Garba, wanda ya wakilci Sufeto-Janar na ‘Yansanda, ya gode wa gwamnan kan wannan taimako.
Ya bayyana cewa hakan wata babbar nasara ce ga tsaron al’umma a Kano.
Ya tabbatar da cewa za su yi amfani da motocin yadda ya dace a dukkanin sassan rundunar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.