Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano ta haramta gudanar da bikin ranar ƙauyawa kuma ta ba da umarnin rufe dukkan wuraren shagulgulan biki a jihar.
Babban Sakataren hukumar, Abba El-Mustapha, ya sanar da wannan a yau Asabar bayan wata sabuwar dokar da majalisar jihar ta zartar kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ita.
- Za A Gudanar Da Taron Tallata Fim Din “Red Silk” A Moscow
- NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC
“Daga yanzu, shirya ko wani biki a ƙarƙashin sunan ƙauyawa Day ko Ranar Kauyawa ya zama haram a ƙarƙashin wannan sabuwar doka,” in ji El-Mustapha, yana mai cewa hukumar ta sami ikon aiki akan dukkan wuraren nishadi da ayyukan DJ a jihar.
Haramcin ya zo ne sakamakon ƙorafe-ƙorafe da malaman addini da al’umma ke yi kan yadda ake gudanar da waɗannan bukukuwan da matasa ke shirya su, waɗanda wasu ke zargi da ingiza halaye marasa kyau.
Hukumomi sun kira ga sarakuna, da jami’an tsaro da Hisbah su taimaka wajen tabbatar da bin wannan umarni. Duk wurin taron da aka yi amfani da shi wajen yin wannan shagali zai fuskanci rufewa ta dindindin da kuma gabatarwa zuwa kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp