Wata jami’a ta hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa da rigakafinsu ta kasar Sin, watau China CDC, ta musanta cewa an samu barkewar wasu cututtuka masu yaduwa a kasar, inda ta jaddada cewa, cututtukan da suka shafi numfashi da ake fama da su a kasar duka wasu sanannun kwayoyin cuta ne ke haifar da su.
A halin yanzu, zazzabi da mura su ne sahun gaba da ke sa mutane ziyartar asibitoci, musamman majinyata masu fama da kwayoyin cutar da suka shafi numfashi, kamar yadda masaniya mai bincike a cibiyar yaki da cututtukan masu yaduwa, Wang Liping ta yi bayani a wani taron manema labarai da hukumar kula da lafiya ta kasar Sin ta gudanar a ranar Lahadi.
Wang ta kara da cewa, bayanai sun nuna cewa, yawan kamuwa da mura bai yi kamari ba a galibin lardunan kasar, kuma yayin da makarantun sakandare da na firamare suka shiga hutun lokacin hunturu, ana sa rai a samu raguwar kamuwa da murar daga tsakiya zuwa karshen watan Janairun da muke ciki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)