Jami’an Hukumar Tsaro ta farin kaya, DSS sun kama wani Musa Abubakar da ake zargi da safarar makamai ga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da suka addabi Jihar Filato da sauran sassan Arewa.
Wannan lamari ya biyo bayan wani rahoton sirri da hukumar DSS ta samu, wanda ya kai ga kama shi a ranar 12 ga Nuwamba, 2025.
Wata majiya daga hukumar DSS ta ce, “Wanda ake zargin ya amsa laifin kerawa da kuma rarraba manyan makamai da harsasai ga ƙungiyoyin mahara da ke da hannu a hare-haren ta’addanci a Jihar Filato da sauran yankunan arewa.
“An kama Abubakar da hannu dumu-dumu da wasu abubuwan fashewa, sinadarai, da kayan aiki, waɗanda jami’an DSS suka kwace,” in ji majiyar.













