Hukumar bunkasa makamashi da hadin gwiwa ta kasa da kasa, GEIDCO a takaice, hukuma mai zaman kanta a birnin Beijing, dake inganta ci gaban makamashi mai dorewa a fadin duniya, ta tsara wani tsarin hada makamashin da ta fito da shi ga nahiyar Afirka.
Daraktan sashen tsare-tsare na cibiyar tattalin arziki da bincike na hukumar Song Fulong, ya bayyana shawarwarin da kungiyar ta gabatar, yayin taron shekara-shekara na kungiyar masu amfani da wutar lantarki na Afirka karo na 57 da ake gudanarwa a babban birnin Malawi na Lilongwe ranar Talata.
Bisa ga gabatarwar da Song ya gabatar mai taken “Bincike da mahangar hadin kan makamashi na Afirka,” GEIDCO na shirin gina hanyoyin hadin gwiwa guda 3 a Afirka, da kuma cimma hadin kai tsakanin yankuna ta hanyar manyan layukan samar da wutar lantarki. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp