Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Alhamis din cewa, a baya-bayan nan, kungiyoyi da cibiyoyin kasa da kasa masu tarin yawa, da suka hada da MDD, da bankin duniya, da asusun bayar da lamuni na duniya IMF, da sauransu, sun nuna fatansu game da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana, wanda ke nuna cikakkiyar imanin al’ummar duniya game makomar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da zama injin, tare da ba da gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya.
Wang Wenbin ya ce, Amurka ta dade tana cin zarafin da darajar dala, da karbar rancen kudi, da turo hauhawar farashin kayayyaki zuwa kasashen duniya, lamarin da ya kawo cikas ga farfadowar tattalin arzikin duniya.
A ranar 7 ga watan Yuni ne, aka gudanar da taron ba da shawarwari kan harkokin tsaro tsakanin Sin da Pakistan da Iran karo na farko a birnin Beijing, fadar mukin kasar Sin.
Wang Wenbin ya ce, kasashen uku sun yi musayar ra’ayi mai zurfi kan yanayin yaki da ta’addanci a yankin, da yaki da ‘yan ta’adda tsakanin iyakokin kasashe da sauran batutuwa, inda suka yanke shawarar gudanar da shawarwari kan harkokin tsaro kan yaki da ta’addanci tsakanin sassa uku kamar yadda aka tsara. (Mai fassarawa: Ibrahim)