Hukumar Ilimin bai-ɗaya ta ƙasa (UBEC) ita ce ta lashe lambar yabo ta Leadership ta Hukumar Gwamnati mafi ƙwazo a shekarar 2024. Hukumar ta a samu ɗinbin nasarori a harkokinta na ilimi, wanda hakan yasa ta zama a sahun gaba wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi a Nijeriya.
Tun lokacin da ya kama aiki a shekarar 2016, babban sakataren hukumar, Dr. Hamid Bobboyi, ya taka rawar gani wajen tsara manufofin da suka inganta harkar ilimi a faɗin Nijeriya.
- Sin Ta Yi Tir Da Matakin Amurka Na Sayarwa Taiwan Makamai
- Jerin ‘Yan Wasa Uku Da Suka Zura Kwallaye 100 A Gasar Zakarun Turai
Jagorancin Dr. Hamid ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da shirye-shiryen da aka tsara don inganta harkokin ilimi ga ƙananan yara a Nijeriya. Yunkurin UBEC na inganta ilimi, an ganshi a fili a cikin tasirin da shirye-shiryentai. A shekarar 2024, hukumar ta kaddamar da wasu muhimman tsare-tsare da zai daƙile ƙalubale a fannin ilmin bai-ɗaya a faɗin ƙasarnan.
UBEC ta faɗaɗa shirinta na samar da makarantu masu amfani na zamani a fadin ƙasar nan. Waɗannan makarantu an zuba musu kayan koyo da koyarwa da na fasahar sadarwa ta zamani (ICT)..A yanzu dai aƙalla akwai kimanin makarantu 37 da suka shafi koyar da ilimin kimiyyar fasahar sadarwar ta zamani (ICT), da suka fara aiki a kowace jiha.
Hukumar UBEC na ci gaba da ganin ta bunƙasa sauran makarantun, waɗanda da yawa daga cikinsu ana dab da kammala aikinsu da tare bai wa malamai horo ta hanyar ware fiye da Naira biliyan 10 a duk shekara don horar da su, don su samu ƙwarewar da ta dace a fannin koyarwa na zamani.
UBEC ta ƙirƙiro wannan tsarin na koyarwar zamani biyo bayan ɓarkewar annobar COVID-19 don haɓaka shirye-shiryenta na koya da ilimin fasahar sadarwa na (ICT), kamar amafani da hanayr koyarwa ta yanar gizo, da suka haɗa da Ajujuwan Google da shafukan karantarwa na yanar gizo, da sauran manhajojin yanar gizo da ke bai wa ɗalibai damar koyo, yanzu duk an haɗe su cikin tsarin koyon ilimi na Nijeriya.
A bana, UBEC ta ƙuduri aniyar samar wa makarantu kayan karantarwa na zamani da intanet, tare da ci gaba da horar da malamai da ɗalibai, don haɓaka amfani da waɗannan kayayyakin karantarwar na zamani.
Haka kuma hukumar ta samu ci gaba sosai a fannin ilimi, inda ta ware kashi biyu na kasafin kuɗinta na shekara, kimanin naira biliyan 2.1, domin tallafa wa yara masu bukata ta musamman tare da kara faɗaɗa hanyoyin ilmantarwa ta yanar gizo a cikin 2024. Wadannan tsare-tsare sun bayar da damar isar da ilimi wurare masu nisa, inda tsohon tsari ba zai iya kai wa ba.
UBEC ta duƙufa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin ilimi, musamman yara mata da masu buƙata ta musamman ta hanyar shirye-shirye da tsare-tsaren da hukumar ta bijiro da su don rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da inganta tsarin mayar da al’umma cikin tsarin koyon ilimi.