Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kasa, Zacch Adedeji ya bayyana cewa, a halin yanzu hukumar ta kammala shirin tunkarar Majalisar Kasa don a samar da dokar da za ta sa ido a kan harkokin ‘yan Kirifto a Nijeriya.
Adedeji ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki tare da’yan kwamitin majalisar dattawa da na wakilai a kan harkokin kudi da aka yi a Legas a makon jiya.
- Kisan Gillar Basaraken Daular Gobir A Hannun Masu Garkuwa Ta Girgiza Al’umma
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Sadarwa
Ya ce, matakin farko shi ne an samar da dokar da za ta sanya ido a kan harkokinsu, shi ya sa kuka ga ‘yan majalisar kasa gaba daya a wannan taron, wannan ne matakin farko, haka kuma ake yi a ko’ina a duniya, in aka samu bullar wani sabon lamari kamar wannan, saboda haka dole ka shirya fuskanta lamarin domin ba za a iya kauce masa ba. Muna shirin sanya ido a kai ta yadda ba zai yi illa ga tattalin arzikin Nijeriya ba.
Ya kuma ce, hukumar ta yi hankoron samar da harajin fiye da na Naira Tiriliyan 19.4 daga bangarori daban daban a shekarar 2024.
A kan wasu haraji kuma kamar ‘stamp duty’, ya ce, “Wasu dokokin haraji da kasar nan ke amfani da su an kafa su ne tun shekarar 1939. A lokacin kuma ba mu da gwamnmatin jihohi da na kananan hukumomi, saboda haka ne shugaban kasa ya kafa kwamitin domin sake nazarin dokokin kasa tare da samar da mafita domin ciyar da kasa gaba.”
Adedeji ya kuma ce, “Zuwa watan Satumba za a gabatar wa da majalisar kasa sabbin doka wanda zai zama matakin farko na daidaita harkokin masu sana’ar Kiripto a Nijeriya.”
“A yau ba za mu iya kauce wa daga harkokin ‘yan kirifto ba, amma kuma abin mamaki shi ne babu wata doka a fadin kasar nan da ta sanya ido a harkokin ‘yan kirifto. Kuma ba za mu iya kawar da ido daga harkokinsu ba.”
A nasa tsokacin, shugaban kwamitin majaliar dattawa a kan harkokin kudi, Sanata Muhammed Musa ya ce, majalisar kasa za ta yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin karfafa hjanyoyin karbar haraji a fadin kasar nan.
“A kan haka aka samu hadin kai tsakanin majalisar dattawa da majalisar wakilai don cimma wannan manufar” in ji shi