A shirye-shiryen hukumar Hisbah ta jihar Zamfara kan habaka al’adu da kula da tarbiyyar Addini, ta hana wasu bukukuwan aure kafin baki, kamar su Kauye Day, Fulani Day, Kamu da Sauran bukukuwan da basu cancanta ba.
Yayin ganawa da manema labarai, Shugaban Hukumar, Sheikh Hassan Umar ya nuna matukar damuwa kan yadda aka kutso da wasu al’adu cikin bukukuwan aure da basu inganta ba a addini.
Domin tabbatar da bin wannan dokar, Hukumar ta kaddamar da kwamitoci guda Uku da za su yi aiki da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an aiwatar da dokar kuma an shawo kan wannan kalubalen.