Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kaddamar da farautar wasu fitattun ‘yan tiktok a Kano su 6 da ake zargi da yin ba daidai ba a manhajar tiktok dinsu da sauran kafafen sada zumunta.
Hukumar ta ce, abubuwan da ‘yan tiktok din suka wallafa a shafinsu ya saba wa dokokinta da ka’idojinta.
- Ba Za Mu Aminta Da Ɗauke Babban Bankin Nijeriya Zuwa Legas Ba – Kungiyar Matasan Arewa
- Mayar Da CBN Legas: Muna Roko A Mayar Da Ma’aikatar Kasuwanci Kano, NNPCL, NIMASA, NPA Zuwa Neja Delta
Wannan na zuwa ne ‘yan watanni bayan da Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya mika goron gayyata ga daukacin mata ‘yan tiktok na Kano domin gudanar da wani zama na tattaunawa.
A yayin taron, hukumar ta bayar da damammaki na gyarawa da karfafawa ’yan tiktok , da suka hada da koyar da sana’o’i da bayar da tallafin karatu domin a nisantar da su daga dabi’u na rashin tarbiyya.
Sheikh Daurawa, a nasa jawabin, ya bukaci dukkan masu sha’awar yin amfani da manhajojin sada zumunta na zamani da su guji yada abubuwan da za su iya haifar da gurbacewar tarbiyya da al’ada a cikin al’umma.
Daga cikin ‘yan tiktok din da Hukumar Hisbah ta kaddamar da farautarsu sun hada da Murja Ibrahim Kunya, Abubakar Ibrahim (G-Fresh), Sadiya Haruna, Ashiru Idris (Maiwushirya), Ummee Shakira, da Hassan Makeup.