Hukumar tara haraji ta kasa, FIRS ta sanar da tara Naira Tiriliyan 12.374 a matsayin kudaden haraji na shekarar 2023, wanda ya zarce Naira tiriliyan 10.7 da hukumar ta yi hasashen tarawa a shekarar.
Da take bayyana alkaluman, daya daga cikin masu gudanarwa ta hukumar, Misis Amina Ado, ta ce, kudaden shigar man fetur ya kai Naira tiriliyan N3.17 na jimillar kudaden da aka karba, wanda ya ke daidai da kashi 25.6 cikin 100, yayin da kudaden da aka tattara ba ta bangaren man fetur ba ya kai Naira tiriliyan N9.2 daidai da kashi 74.4 cikin 100.
- Gwamnatin Taraba Ta Haramta Hawa Babura A Jalingo
- Tinubu Ya Tsige Nami, Ya Maye Gurbinsa Da Adedeji A Hukumar Tattara Haraji Ta FIRS
Hukumar tun a farko ta sake nazarin karawa kan kudin harajin farko na Naira Tiriliyan 10.7 na shekarar 2023 zuwa fiye da Naira Tiriliyan 11.5 bisa la’akari da karuwar canjin kudin, wanda hakan ya nuna cewa, an samu karin fiye da Naira biliyan N817 akan sabon harajin da aka yi nazari akai na Naira Tiriliyan N11.5.
FIRS a bana na da yunkurin tattara harajin Naira tiriliyan N19.4, kuma shugaban hukumar, Dokta Zacch Adedeji, ya ce za a iya cimma wannan burin ta hanyar amfani da ingantaccen tsarin tattara haraji a cikin yanayin tattalin arziki mai inganci.