Hukumar shirya jarabawar manyan makarantu ta kasa ta bayyana cewar ta tura kudi Naira bilyan 6 zuwa asusun ajiyar gwamnatin tarayya bayan da aka kammala jarabawar shigaba manyan makarantu (UTME) ta shekarar 2024.
Mai bada shawaran harkoin sadarwa na hukumar, JAMB, Dakta.Fabian Benjamin,shi ne wanda ya bayyana hakan kamar yadda sanarwar data fito ta kafar sadarwar hukumar da aka lika a allon sanarwar hukumar ranar Litinin..
- NAF Ta Tarwatsa Ma’ajiyar Makamai Da Ke Shiroro A Neja
- NAFDAC Ta Rufe Babban Kantin ‘Yan China A Abuja Saboda SaÉ“a Dokoki
Hukumar ta bayyana ta samu kudaden shiga d a suka kai Naira bilyan 22,996,653,265.25 ta kuma kashe Naira bilyan 18,198,739,362.68 wajen shirya jarabawar (UTME),ta biya masu bada hanyar kafar sadarwa, da suka hada da kudaden bashin da ma’aikata suke bi da suka kai Naira bilyan 2,119,571,022.88.
Shekarar 2024, kamar yadda hukumar ta bayyana shekarar ce wadda JAMB cin garavasar tsare- tsaren da ta yi wadanda kuma tuni ta fara aiwatar da su.
Har ila yau sanarwar ta bayyana inda yadda hukumar tayi ta fadi- tashi har aka kai ga halin da ake ciki a shekarun da suka gabata,wanda tuni aka yi niyyar tafiyar da al’amura cikin gaskiaya da adalci, yin abu babu wani voye- voye, a fili domin kowa ya gani, saboda kuwa tun a shekarar 2017 aka fara yin hakan, tana bayyana irin kudaden shigara da aka samu kowane mako da kuma abinda ka kashe saboda al’umma su gani da kuma ji.
Yayin da ake jiran yadda shekarar 2025, zata kasance hukumar har yanzu hukumar tana nan kan bakanta na ci gaba dayin al’amuranta kamar yadda ta fara na yin bayanin halin da ake ciki dangane da kudaden da suka shigo mata an dai samu kudaden shiga da suka kai Naira tiriliyan 22,996,653,265.25.