Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta samu nasarar ceto mutum 135 da dukiyar da aka kiyasta kudin su ya kai Naira Miliyan 34.6 a aukuwar gobarar da aka samu a watan Yuni har sau 42.
Bayanin haka yana kunshe ne a cikin takardar sanawar da jami’in watsa labarai na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a Kano.
- Gobara Ta Kone Shaguna 42 A Jami’ar ATBU Bauchi
- Hajjin Bana: Saudiya Ta Hana Amfani Da Gas Din Girki A Lokacin Aikin Hajji
Ya kuma kara da cewa, mutum 24 sun mutu, yayin da wutar ta kona kayyakin da aka akiyasta ya kai na Naira Miliyan 13 a cikin lokacin da ake magana.
Daga nan ya ce, sun samu kiran gaggawa har sau 77 yayin da aka yi musu kiran bogi har sau 17 daga al’umma jihar.
Jami’in watsa labarai na hukumar ya kuma danganta tashin gobarar da ake samu ga sakaci da ake yi da kayan wuta a gidajen mutane.
A kan haka ya shawarci al’umma su yi kaffakaffa wajen amfani da wutar lantarki musamman a wannan lokaci na bikin sallah da ake fuskanta.
Ya kuma shawarcesu da su lizimci dokokin hanya a yayin bukuwan sallah.