Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta ceto wata mata da ’ya’yanta maza biyu bayan sun maƙale a gini da ya rufta a Makwarari, ƙaramar hukumar Kano Municipal, a jiya Juma’a.
Iftila’in ya shafi wani gini ne mai hawa daya mai girman ƙafa 30 da ƙafa 40. An bayyana mutanen da abin ya shafa da sunayen Balaraba Abba, mai shekara 35, da ’ya’yanta maza, Abdulnasir Jilani, mai shekara 12, da Abdullahi Jilani, mai shekara 9.
- Ma’aikaci Ya Mayar Da Dala 10,000 Da Ya Tsinta A Cikin Jirgi A Kano
- KANSIEC Ta Sauya Lokacin Zaben Kananan Hukumomin Kano Zuwa Oktoba
Jami’in hulɗa da Jama’a na hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa. Ya bayyana cewa hukumar kwana-kwanan ta samu kiran gaggawa kusan karfe 9:30 na safe daga wani ma’aikaci, Ibrahim Isah, yana sanar da su game da ruftawar ginin. Nan take aka tura ma’aikatan ceto zuwa wurin domin gudanar da aikin ceto.
Sanarwar ta bayyana cewa an ceto mutanen da abin ya shafa kuma su na raye har ma an kai su asibitin kwararru na Murtala Muhammed domin a ba su magani. Babu wani bayani da aka bayar dangane da halin da lafiyarsu ke ciki a yanzu.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin ruftawar ginin.
Za a iya samun ƙarin bayani yayin da binciken ke ci gaba.