Daraktan Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NCS) ta tara jimillar kuɗin shiga da ya kai biliyan ₦658.6 a watan Satumba 2025, wanda ke nuna ci gaba mai kyau a sauya sauyen tsarin kuɗaɗen gwamnati da kuma sakamakon gyare-gyaren da ake gudanarwa.
Issa-Onilu ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da ake gudanarwa duk wata, wanda NOA ke jagoranta tare da hukumomin tsaro, paramilitary, da masu kula da harkokin tattalin arziki.
- Sojoji Sun Kai Hare-hare 261, ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 1,950 A Watan Agusta – NOA
- Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA
Ya ce wannan nasara ta nuna rawar da hukumar Kwastam ke takawa wajen aiwatar da tsarin sauya tattalin arziƙin ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Bashir Adewale Adeniyi. “A watan Satumba, Hukumar ta tara jimillar kuɗaɗen shiga na ₦658,605,400,392, wanda ke nuna ƙarfin tsarin tattalin arziƙin hukumar duk da irin sauye sauyen da ake yi,” in ji shi.
Issa-Onilu ya ce hukumar ta gudanar da muhimman shirye-shirye a watan Satumba, ciki har da ganawar da musayar dabaru da ƙungiyar masana’antu ta MAN, domin ƙarfafa dangantakar kasuwanci, da inganta tsare-tsare, da ƙara bunƙasa masana’antu. Haka kuma, hukumar ta gabatar da manhajar biyan buƙata ta bai ɗaya (One-Stop-Shop) domin rage jinkirin fitar da kaya da kuma hana tangarda a tashoshin kasuwanci.
A ɓangaren tsaro, Issa-Onilu ya bayyana cewa sashin Federal Operations Unit (FOU) Zone A ya cafke makamai, da jiragen leƙen asiri (industrial drones), da wasu haramtattun kayayyaki a yankin kudu maso yamma, wanda ke nuna jajircewar hukumar wajen kare iyakokin ƙasa da hana fataucin haramtattun kaya.
Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki.
A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana kafa sabon ma’auni na kwarewa da ingantaccen aiki a tsarin gwamnati.