A ranar Alhamis Hukumar Kwastom a Nijeriya ta fara sayar da shinkafar da aka kwace ga ‘yan Nijeriya a Legas.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa Hukumar ta shirya sayar da shinkafa kilogiram 50 kan Naira 20,000 domin rage tsadar farashin shinkafa da kuma dakile tabarbarewar tattalin arzikin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
- Kwastom Ta Kama Haramtattun Kayan Naira Biliya 1.17 Cikin Wata 8
- Kwastam Za Ta Raraba Wa ‘Yan Nijeriya Shinkafa Da Sauran Kayan Da Ta Kwato
Da yake ganawa da manema labarai a Legas a lokacin da aka fara sayar da kayayyakin, Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce za a fara sayar da shinkafar ne a duk wuraren da ake samun kayayyakin da aka kama daga ranar Juma’a 23 ga Fabrairu, 2024 N10,000 akan kowane 25kg da N20,000 akan 50kg.
Sai dai ya bayyana cewa za a sayar da kayayyakin ga manukata ‘yan Nijeriya ne kadai kuma za su yi aiki tare da rundunar ‘yan sanda don tabbatar da ingancin aikin.
A cewarsa, sharuddan sun hada da samun tabbataccen lamba katin dan kasa ta (NIN) da kuma wadanda za su ci gajiyar sayar da kayan sun hada da kungiyoyin addini da dai sauransu.
Hukumar Kwastam, ta ce da zarar an samu irin kayan a shagunan kasuwanci, za a kama za kuma a rufe shagon tare da gurfanar da mai shagon a gaban kotu.