Ran 22 ga wata, shahararren dan jarida mai gudanar da bincike kwa-kwaf Seymour Hersh ya sake wallafa wani bayani a shafukan sada zumunta, yana mai cewa, hukumar leken asiri ta Amurka ta CIA ta kirkira tare da yada labaran karya kan bututun jigilar iskar gas na “Nord Stream”, wai kungiyar dake goyon gwamnatin Ukraine ne suka kai hari da bama-bamai kan bututun “Nord Stream”, don rufe gaskiyar maganar. Wannan labarin karya ne.
A wannan karon, Seymour Hersh ya ba da cikakkun shaidu da ma bayanai kan lamarin. Rahoton ya ambato maganar majiyoyi na diflomasiya na cewa, yayin ziyarar da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ziyarci Amurka a farkon wannan wata, ya tattauna da shugaban Amurka Joe Biden kan yadda za a kai hari kan “Nord Stream”. Daga baya, hukumar leken asiri ta Amurka CIA, ta karbi aikin hadin kai da takwararta ta Jamus(BND) don shirya labarin karya kan lamarin, a kokarin boye gaskiyar batun.
Idan har labarin da Seymour Hersh ya fada gaskiya ne, to dole ne MDD ta jagoranci cikakken binciken kasa da kasa kan lamarin, don gano gaskiya. (Amina Xi)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp