Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Brig. Janar Mohammed Marwa (mai ritaya) ya ce an kama mutane 14,480 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban 2024.
Marwa, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a lokacin da yake zantawa da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi, wadanda suka kai ziyarar aiki a hedkwatar hukumar ta NDLEA da ke Abuja, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da hannu wajen safarar nau’ukan miyagun haramtattun kwayoyi kimanin kilo miliyan 2.4 a tashoshin jiragen ruwa, filayen jirgin sama, iyakokin kasa da kuma cikin gundumomi a fadin kasar.
- Sin Ta Jaddada Kudurinta Na Kara Inganta Daidaito Da Tsaro A Tekun Guinea
- Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Shari’a Da Majalisa Su Yi Aiki Tare Kan Dokar Haraji
Ya ce, duba da ayyukan da hukumar ta yi a cikin watanni 10 da suka gabata, “za mu iya cewa, muna kan turbar samun nasara fiye da wacce aka samu a ayyukan da hukumar ta yi a shekaru uku da suka gabata.”
Yayin da yake yabawa ‘yan majalisar kan goyon bayan da suka ba su, Marwa ya bukace su da su ci gaba da taimaka wa ayyukan hukumar domin cimma nasara.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin majalisar kan yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi, Hon. Abass Adigun, ya yabawa shugabanni da ma’aikatan hukumar bisa jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu duk da kalubalen da suke fuskanta.