Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta bayar da tabbacin cewa, aikin samar da sauki a hada-hadar jigilar kaya na kasa wato NSWP, za a kammala shi a zango na daya a 2026.
Wannan na zuwa ne, bayan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da a zamanantar da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Apapa da ta Tin Can Island.
- Har Yanzu Manyan ‘Yan Wasa Suna Son Buga Wasa A Manchester United – Amorim
- Masana Sun Bayyana Yadda Yakin Neman Zaben 2027 Ke Barazana Ga Harkokin Tafiyar Da Gwamnati
Shugabanta Dakta Abubakar Dantsoho ya sanar da haka a yayin da yake yiwa baki jawabi a yayin kadammar da kwamtin tabbatar da ingnaci da za su sa ido kan ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da kuma na Hukumar Kwastam ta Kasa, wato PCEC da aka gudanar a ranar Alhamis a jihar Legas.
Cibiyar samar da kyakyawan yanayin yin kasuwanci na Fadar Shugaban Kasa da hadaka da NPA ne, suka shirya taron kaddamarwar,
“Ana sa ran a zangon farko na 2026, aikin na NSWP zai fara fara aiki wanda tuni, Fadar Shugaban Kasa ta amince da kwangilar domin a wanzar da aikin,” Inji Dantsoho.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, za a rinka gudanar da ganawa akai-akai da masu ruwa da tsaki domin gudanar da hada-hadar kasuwanci a cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar a cikin nasara.
Ya sanar da cewa, zuba hannun jari a kayan aiki Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, samar da kayan aiki na fasahar zamani da sauransu, za su taimaka wajen kara habaka kasa da kuma gudanar da ayyuka, a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
Dantsoho ya kara da cewa, kayan aikin da ke a musamman Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da Tin Can Island, sun jima ana yin amfani da su a kasar nan, wadanda kuma akwai bukatar a yi masu garanbawul.
“Yau kimanin shekaru 48 ke nan, da kafa Tashar Jirgin Ruwa ta Tin Can Island, inda kuma ta Apapa ta kai kimanin shekaru 100, amma har yanzu, ba a yi masu wani garanbawul ba,” A cewar Dantsoho.
Sai dai, ya sanar da cewa, amincewar kwanan baya da Gwamnatin Tarayya ta yi na a yiwa daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar garanbawul, hakan zai kara taimakawa wajen gudanar da ayyuka a Tashoshin.
A bangaren kimiyya Shugaban ya bayyana cewa, Hukumar na ci gaba da aiki kafada da kafada da kungiyar kula da harkokin teku ta kasa da kasa wato IMO, domin yin amfani da tsarin PCS, duba da cewa, inda ya alakanta aikin na NSWP, a matsayin wani banban ginshiki.
Dantsoho ya jadda cewa, tsarin na PCS, zai kawar da yin amfani da takardu, da kuma yin shisshigi, wanda hakan zai kuma kara tabbatar da kawar da duk wata badakala da za ta iya kunno kai da rage tsada da kuma kara samar da kudaden shiga.
“Hukumar ta NPA kadai, ba za ta yi cimma burin da ta sanya a gaba sai ba, sai an hada karfi da karfe kuma kara tabbatar da inganci, abu ne da ya karade kowanne fanni, matukar muna son kara samar da karin kudaden shiga wadanda za su yi daidai da na fadin duniya ,” , A cewar Dantsoho.
A na ta jawabin, Darakta Janar ta Kwamitin Gudanar da Muhalli na Kasuwanci na Shugaban kasa (PEBEC) Princess Zahrah Mustapha Audu ta bayyana cewa, inganganta ayyukan, za su taimaka wajen rage cunkson Jiragen Ruwa a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
A cewarta, an kaddmar da Kwamitin ne, domin a samar da sauye-sauye rashin damar da ba a samu a fannin ayyukan Tashihin da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp