Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Nijeriya (NRC) ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a kan layin dogo na Abuja zuwa Kaduna biyo bayan hatsarin da jirgin ya yi a ranar Talata.
Manajan Darakta na NRC, Kayode Opeifa ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja bayan faruwar lamarin.
Opeifa ya jaddada cewa, an dakatar da zirga-zirgar jiragen har sai an kammala bincike da kuma tabbatar da tsaro, tare da bayyana cewa an shirya mayar da kudade ga duk fasinjojin da wannan lamari ya shafa.
Opeifa ya kara da cewa, tuni tawagar kwararru daga Hukumar, jami’an Hukumar Binciken Tsaro ta Nijeriya (NSIB) da sauran hukumomin da abin ya shafa suka isa wurin domin gano musabbabin wannan matsala da kuma tabbatar da daukar matakan kariya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp