Hukumar Raya Arewa Maso Yamma (NWDC) ta sanar da soke shirin tallafin karatu na ƙasashen waje da ta gabatar kwanan nan, bisa wani sabon umarni daga gwamnatin tarayya na ba da fifiko ga ci gaban ilimi a cikin gida.
Sanarwar ta fito ne a shafin X na hukumar, inda ta bayyana cewa shawarar ta biyo bayan sauyin manufar gwamnatin tarayya na inganta cibiyoyin ilimi na gida da kara ƙarfafa ilimi a ƙasar.
- Fannonin Da Xi Jinping Ya Lura Da Su A Ziyararsa A Arewa Maso Gabashin Sin
- Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Fara Taronsu Karo Na 11 A Yobe
“NWDC ta sanar da soke neman tallafin karatu na ƙasashen waje, bisa sabon umarnin gwamnatin tarayya na ba da fifiko ga ilimi a Nijeriya,”
in ji sanarwar.
Hakan ya zo ne bayan sanarwar da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta fitar a ranar 7 ga Mayu, 2025, wanda daraktar yaɗa labarai, Mrs. Folasade Boriowo ta sanya hannu, inda gwamnati ta jaddada mayar da hankali kan inganta ingancin ilimi a cikin ƙasar da rage dogaro ga shirye-shiryen karatu na ƙasashen waje.
Ko da yake NWDC ba ta bayyana wani madadin shirin karatun ƙasashen wajen ba, ta tabbatar da cewa za ta ba da wata sana’arwar kan sabbin shirye-shiryen raya yankin nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp