• English
  • Business News
Sunday, October 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukuncin Ganin Watan Ramadan Na Hadisin Kuraibu Da Fatawar Malamai

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
3 years ago
in Labarai
0
Hukuncin Ganin Watan Ramadan Na Hadisin Kuraibu Da Fatawar Malamai
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A’uzu billahi minash shaidanir rajim, bismillahir rahmanir Rahim. Allahumma Salli ala Sayyidina Muhammadin Alfatihi lima uglika wal khatimi lima sabaka nasiril hakki bil hakki, wal hadi ila siradikal mustakim wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim. 

Wa radiyallahu an as’habi rasulullahi (SAW), wa la haula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim. Ya himmatash Sheikh, ihdirilana bi hazal mahdari wal ta’adifi binazaratin ta’ati lana bizzafari.

  • Dan Majalisar Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Fita Yakin Neman Zabe A Bauchi
  • EFCC Ta Gurfanar Da Farfesa A Gaban Kuliya Bisa Zargin Damfarar N1.4bn

Alhamdu lillah. Masu karatu, a makon da ya gabata mun ce za a wannan makon za mu tabo bayani a kan yanayin kankan da kai na Manzon Allah (SAW), sai dai saboda karatowar duba watan azumin Ramadan, muka ga ya dace mu tabo batunsa. Wancan kuma cikin yardar Allah bayan kammala azumi za mu ci gaba da shi.

Mun gode Allah da ya nuna mana karatowar sabon wata na Ramadana, wata mai alkairi, mai albarka, wata mai dukkan wani abu na falala da za a fada, muna fata wurin Allah ya azurta mu da azumtarsa, Allah ya buda wa al’ummar musulmi da abin da za a ci, a sha, Allah ya dauke mana dukkannin musifu albarkacin watan.

Muslim ya fitar da Hadisi daga Abdullahi bin Umar ya ce manzon Allah (SAW) ya yi magana a kan azumi, har sai da ya yi ishara da hannunsa, yana nuni da yatsun hannayensa guda goma, ya yi nuni da su sau biyu, na ukun sai ya kulle babban yatsansa, yana nufin tara (goma sau biyu, sai tara), Annabi SAW yana nufin in kuka yi azumi 29 aka ga wata ku sha ruwa, (Sumu li ru’uyatihi, wa afdiru li ru’uyatihi, wa’in summa alaikum fakdiru salasina – ku yi azumi in an ga wata, ku sha ruwa in an ga wata, idan ba a ga wata a 29 ba, ku kudurce yin Talatin).

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

Atiku Ya Zargi Tinubu Da Fifita Ziyarar Siyasa A Maimaikon Ta Waɗanda Rashin Tsaro Ya Shafa 

Wurin maganar ganin wata, kowacce kasa ana yi mata hukunci ne da Sarkin Musulmi, duk masarautun da ke karkashinsa sai su ba shi rahoton ganin watan, in wancan garin ba su gani ba wani garin za su gani, in Sarki ya yarda, azumi ya zama farilla a kan duk musulmin garin amma in duk garuruwan ba a gani ba sai a shirya cika talatin.

Hadisi yazo daga Abdullahi bin Umar cewa “Inna ummatan ummiyyatan – mu al’umma ce ba’umma, yana nufin a yanzu ba su iya yin hisabi ba.”

Har ila yau yana daga hukuncin shari’a, ba a fara azumi da kokwanto, misali ka kwanta bacci sai ka kudirce a ranka cewa in an bayyana ganin wata ina bacci, zan tashi da azumi. Mun gode Allah, yanzu sabida na’u’rar zamani da wuri ake sanar da ganin wata.

Lamarin ganin watan Ramadana abu ne mai sauki, sabida galibin Malamai da Shehunnanmu na kasa da waje baki daya suna kan Hadisin Kuraibu da yake cewa “Kowacce kasa da ganin watanta, misalin kasar: Nijer da Ghana, Mali, Togo da dai sauransu duk suna da Sarkin Musulmi kuma shi zai ayyana ganin watan.

Amma kuma, in Nijer suka ga watan Ramadana, Sarkin Musulmin Nijeriya in yaga dama zai iya cewa na ga wata da ganin watan Nijer sabida dare da lokutan kasashen duk iri daya ne. Sai dai ban da kasar da lokutansu ba iri daya ba ne – ra’ayin wasu malamai kenan.

Amma a wannan zamani na kimiyya da fasaha, Allah shi ne zamani. Annabi ya ce ba ma Hisabi, ba ma Rubutu (ba wai ya hana ba ne) Littafinsa ne ma ya yi nuni da a yi Karatu “Ikra’a” Allah kuma ya yabi masu Rubutu “Bi’aidi safarah, kiramin bararah” sabida muhimmancin Karatu da rubutu, a ranar yakin Badar, Annabi SAW ya yanke wa duk fursunoni fansa amma ya ce duk wadanda suka iya karatu da rubutu su karantar da yaran Madina, wannan shi ne fansarsu.

Allah ya kawo Kimiyya da fasaha da za a iya ganin abin da ido ba zai iya gani ba daga nesa (Telescope) sabida haka duk duniyar Malaman Musulunci suka yi fatawa cewa yanzun in Makkah ta ga watan Ramadana to duk Musulmi su dauki niyyar azumin.

In Sarkin Musulmi ya ga dama ya yi amfani da hadisin kuraibu, tafiyar iyaye da kakanni cewa kowacce kasa da ganin watanta, Sarkin Musulmi ya yi dai-dai, in ya amshi sabuwar fatawa, sabida Hadisin “Sumu li ru’u’yatihi, wa afdiru li ru’u’yatihi – ku yi azumi in kun ga wata sannan ku ajiye in kun ga wata.” Hadisin ya nuna cewa Annabi SAW ya hade Jama’arsa duka gaba daya.

In an ce Makkah, kar ka kalli wadanda suke cikin garin, ka yi amfani da garin, shi ne wanda Annabi ya zauna a ciki, tushen Addinin Musulunci.

Garin da ba su da dare, kullum rana ce, su kaddara wata, su yi amfani da lokaci, a tsakiyar rana amma lokacin sahur ne ko kuma a tsakiyar rana amma lokacin shan ruwa ne.

In wani musulmi ya ga wata amma Sarkin Musulmi bai amsa maganarshi ba, to shi wanda ya ga watan azumin ya hau kanshi, sai ya azumci azumin a boye sabida girmama hukuma. Addini ya hana Jama’a ta zauna ba shugabanci.

Hadisin kuraibu, tulin Malamai da Shehunnai suna kan wannan Hadisin kuma wayayyu ne sun yarda da zamani.

Hadisin Kuraibu, Muslim ne ya ruwaito shi kuma ingataccen Hadisi ne, Ummul Fadli binti Haris, Matar Abbas dan Abdulmudallib ce ta aiki Kuraibu Sham, wajen Mu’awiya. Kuraibu yake cewa, bayan na isar da sakonta ina Sham, sai azumi ya riske ni ina can, mun ga jinjirin watan Ramadana ranar Alhamis da dare, bayan na dawo Madina, sai Abdullahi dan Abbas ya yi mun zance kan watan, ya tambaye ni yaushe muka ga watan Ramadana a Sham, sai na ce masa ranar Alhamis da dare, sai ya ce min kai ma Allah ya azurtaka da ganinshi? Na ce masa eh, Jama’a da dama sun gan shi, har Kalifa Mu’awiya ma ya yi Azumi, Abdullahi dan Abbas ya ce masa amma mu sai daren Asabar muka ganshi, kuma za mu ci gaba da azumi har sai mun yi 29 ko 30, Kuraibu ya ce masa shin ba za ka wadatu da ganin wata da azumin Khalifa ba, Abdullahi ya ce a’a, ba zan wadatu da ganinsu ba, haka Annabi (SAW) ya umurce mu, kowacce al’umma da ganin watansu.

Wannan Hadisi ingatacce, galibin malamai suna kan shi amma malamai na zamani masu ilimi da fahimta sun tafi cewa tun da Allah ya kawo wadannan ci gaba na kimiyya da fasaha, ba laifi in Sarkin Musulmi ya yarda da ganin watan Makkah ya ce al’ummar Musulmi na duniya su tashi da azumi a rana daya.

An karbo daga Hafsatu Ummul Muminina ta ce Manzon Allah SAW ya ce “Duk wanda bai yi niyyar Azumi ba kafin Asubah, bai da azumi”

Ba laifi, mutum zai iya kudurce niyyar yin azumin ramadana 29 ko 30 a daren azumin farko bayan an sanar da ganin watan ko kuma ya kudurce niyyar azumin ko wacce rana na daga watan ramadana din. Amma ka kwanta bacci da nufin cewa in an ga watan zan ci gaba da azumi in ba a gani ba shikenan, hakan shari’ah ba ta yarda ba.

Allah ya ba mu damar azumtar wannan azumin gabaki daya, Allah ya buda wa ‘yan`uwa musulmin Duniya da abin da za su ci su sha, Allah ya bai wa kasarmu Nijeriya zaman lafiya. Allah ya saka wa iyayenmu na Zawiyya da alkairi wanda da albarkarsu da karfin Allah muke gudanar da wannan lamarin.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: RamadanWatan Azumi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shekara 3 Da Bullar Korona: Yadda Ayyukan Duba-gari Suka Taimaka A Dakile Cutar A Nijeriya —Dakta Yakubu

Next Post

Rikicin Zabe: Jihohin 7 Da Idanuwa Ke Kansu A Zaben Gwamnoni

Related

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun
Labarai

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

50 minutes ago
Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku
Labarai

Atiku Ya Zargi Tinubu Da Fifita Ziyarar Siyasa A Maimaikon Ta Waɗanda Rashin Tsaro Ya Shafa 

2 hours ago
Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 
Labarai

Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 

2 hours ago
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Haɗa-baki Kan Sace Mai Anguwa A Kano

5 hours ago
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Manyan Labarai

Al’ummar Sokoto Sun Koka Kan Yadda Hare-haren Lakurawa Ke Kara Ta’azzara

7 hours ago
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram
Manyan Labarai

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

20 hours ago
Next Post
Rikicin Zabe: Jihohin 7 Da Idanuwa Ke Kansu A Zaben Gwamnoni

Rikicin Zabe: Jihohin 7 Da Idanuwa Ke Kansu A Zaben Gwamnoni

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

October 5, 2025
Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku

Atiku Ya Zargi Tinubu Da Fifita Ziyarar Siyasa A Maimaikon Ta Waɗanda Rashin Tsaro Ya Shafa 

October 5, 2025
Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 

Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 

October 5, 2025
Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

October 5, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Haɗa-baki Kan Sace Mai Anguwa A Kano

October 5, 2025
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

Al’ummar Sokoto Sun Koka Kan Yadda Hare-haren Lakurawa Ke Kara Ta’azzara

October 5, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.