Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta baiwa al’ummar jihar tabbacin samun kariya a kodayaushe musamman a lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa ranar Juma’a.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Hussaini Gumel ne ya bayar da wannan tabbacin yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a ranar Alhamis.
- 2027: Atiku, Kwankwaso Da Obi Na Shirin Kafa Babbar Jam’iyyar Adawa – Pat Utomi
- Bangaren Layin Dogo Na Sin Ya Yi Jigilar Fasinjoji Mafi Yawa A 2023
Gumel ya ce, rundunar ta samar da matakan tsaro da za su bai wa mazauna jihar damar gudanar da sana’arsu ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyinsu ba.
Ya ce rundunar tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro a jihar don tabbatar da cewa ba a samu matsala ba kafin da kuma bayan hukuncin kotun kolin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp