Bakin TAJBank, bankin da ake a kan gaba a Nijeriya wajen aiki da kimiyya da fasaha da ke gudanar da harkokinsa ba tare da bayar ko karbar ruwa ba ya sake cirar tuta inda ya zama zakara a cikin watanni shida na farkon shekarar 2023.
Haka kuma masu binciken kudaden bankin sun bayar da sanarwa cewa, bankin ya samu gagarumin ribar da ta kai na Naira Biliyan N6.019 wanda wannan ne riba mafi girma da aka samu a bangaren bankuna a cikin wannan lokacin da ake magana.
- Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Dukkan Lambobin Zinare Na Wasannin Nutso A Gasar Wasannin Kasashen Asiya
- Me Ya Sa Aka Kasa Shawo Kan Matsalar Hare-haren Bindiga A Kasar Amurka?
Wannan nasarar yana zuwa ne bayan kasa da wata 6 da bankin ya ba masu hannun jarinsa kudade masu kauri a karshen shekarar kudi ta 2022, wannan kuma na zuwa ne kasa da shekara 3 da shigarsu fagen harkokin bankunan kasar nan kuma hakan wani abu ne da babu wata bankin da ta taba samu a tsawon tarihin harkar banki na shekara 100 a Nijeriya.
TAJBank ya kuma kafa tarihi a farkon wannan shekara a matsayin kamfanin hada-hadar kudi na farko da ya bayyana mallaka kaddarar ‘Sukuk Bond’ na Naira Biliyan 100 a bangaren hada-hadar kudaden kasashen wajen Nijreriya.
Haka kuma kididdigar yadda bankin ya gudanar da harkokinsa ya nuna cewa, shi ne a kan gaba wajen fitar da sabbin hanyoyin bayar da bashi mara ruwa inda a zangon farko na shekarar 2023 aka nuna cewa, sun samu riba da kaddamar da kaddarori da suka kai na Naira Biliyan 212.021 a watan Disamba na shekarar 2022 zuwa Naira biliyan 335.017 har zuwa karshen watan Yuni na shekarar 2023, karuwar ya zama daida da kashi 58 ta kuma samu karin kudin shiga da ya kai kashi 67 daga abin da ta samu na naira biliyan 136.149 a karshe watan Disamba 2022 zuwa naira Biliyan 227.031 a karshen watan Yuni na wannan shekarar.
Wasu nasarorin da bankin ya samu a zangon farko na shekarar 2023 sun hada da yadda hada-hadar bankin ya karu da kashi 62 daga naira biliyan 78.235 da aka samu a watan Disamba 2022 zuwa Naira Biliyan 126.725 a zangon farko na shekarar 2022; yayin da kaddarar bankin ya tashi da kashi 88 daga Naira biliyan 19.135 a watan Disamba 2022 zuwa naira biliyan 36.706 a farkon zangon shekarar 2023.
A jawabinsa a kan wannan nasarar da bankin ya samu a daidai wannan lokacin, shugaban Bankin, Mista Hamid Joda, ya ce, wannan nasarar ya samu ne sakamakon sabbin hanyoyin gudanar da aiki na zamani tare da samar da kwararrun ma’aikata masu mu’amala da abokan huldarmu yadda ya kamata.
Ya kara da cewa, wannan nasarar yana nuna cewa, aiki tukuru na da rabarsa kamar yadda muka tsayu a tsawon shekara uku. Babban burinmu shi ne abokan huldarmu, muna kuma kokarin gamsar da su ta hanyar amfani da dukkan kokarinmu don bayyana wa duniya cewa sune a gabanmu, mun dauki hanyar gudanar da harkokin banki ba tare da ruwa ba.
A takaitaccen jawabinsa, daya daga cikin wanda suka kirkiro da bankin, Mista Sherif Idi, ya danganta nasarar da suka samu ga masu hannun jari da abokan huldar bankin, ya kuma kara da cewa, “Muna godiya ga abokan huldar mu da masu hannun jarinmu wadanda sune suke zaburar da mu a nasarar da muke samu zuwa yanzu.
“Ina mai tabbatar muku da cewa, hukumar gudanarwa TAJBank da ma’aikatanta za su ci gaba da kare bukatun ku a dukkan harkokin bankin saboda yadda muka muhimmantar da ku”, in ji shi.