ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Huldar Banki Da Babu Ruwa: Bankin TAJ Ya Samu Ribar Naira Biliyan 6 A Zangon Farko

by Bello Hamza
3 years ago
Taj

Bakin TAJBank, bankin da ake a kan gaba a Nijeriya wajen aiki da kimiyya da fasaha da ke gudanar da harkokinsa ba tare da bayar ko karbar ruwa ba ya sake cirar tuta inda ya zama zakara a cikin watanni shida na farkon shekarar 2023.

Haka kuma masu binciken kudaden bankin sun bayar da sanarwa cewa, bankin ya samu gagarumin ribar da ta kai na Naira Biliyan N6.019 wanda wannan ne riba mafi girma da aka samu a bangaren bankuna a cikin wannan lokacin da ake magana.

  • Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Dukkan Lambobin Zinare Na Wasannin Nutso A Gasar Wasannin Kasashen Asiya
  • Me Ya Sa Aka Kasa Shawo Kan Matsalar Hare-haren Bindiga A Kasar Amurka?

Wannan nasarar yana zuwa ne bayan kasa da wata 6 da bankin ya ba masu hannun jarinsa kudade masu kauri a karshen shekarar kudi ta 2022, wannan kuma na zuwa ne kasa da shekara 3 da shigarsu fagen harkokin bankunan kasar nan kuma hakan wani abu ne da babu wata bankin da ta taba samu a tsawon tarihin harkar banki na shekara 100 a Nijeriya.

ADVERTISEMENT

TAJBank ya kuma kafa tarihi a farkon wannan shekara a matsayin kamfanin hada-hadar kudi na farko da ya bayyana mallaka kaddarar ‘Sukuk Bond’ na Naira Biliyan 100 a bangaren hada-hadar kudaden kasashen wajen Nijreriya.

Haka kuma kididdigar yadda bankin ya gudanar da harkokinsa ya nuna cewa, shi ne a kan gaba wajen fitar da sabbin hanyoyin bayar da bashi mara ruwa inda a zangon farko na shekarar 2023 aka nuna cewa, sun samu riba da kaddamar da kaddarori da suka kai na Naira Biliyan 212.021 a watan Disamba na shekarar 2022 zuwa Naira biliyan 335.017  har zuwa karshen watan Yuni na shekarar 2023, karuwar ya zama daida da kashi 58 ta kuma samu karin kudin shiga da ya kai kashi 67 daga abin da ta samu na naira biliyan 136.149 a karshe watan Disamba 2022 zuwa naira Biliyan 227.031 a karshen watan Yuni na wannan shekarar.

LABARAI MASU NASABA

Kano Ta Tara Harajin Naira Biliyan 102 A Shekarar 2025, Ta Zama Jiha Ta Farko A Arewa

Samar Da Kayayyakin Cikin Gida Na Da Muhimmanci Wajen Ƙarfafa Tattalin Arziki – Dangote

Wasu nasarorin da bankin ya samu a zangon farko na shekarar 2023 sun hada da yadda hada-hadar bankin ya karu da kashi 62 daga naira biliyan 78.235 da aka samu a watan Disamba 2022 zuwa Naira Biliyan 126.725 a zangon farko na shekarar 2022; yayin da kaddarar bankin ya tashi da kashi 88 daga Naira biliyan 19.135 a watan Disamba 2022 zuwa naira biliyan 36.706 a farkon zangon shekarar 2023.

A jawabinsa a kan wannan nasarar da bankin ya samu a daidai wannan lokacin, shugaban Bankin, Mista Hamid Joda, ya ce, wannan nasarar ya samu ne sakamakon sabbin hanyoyin gudanar da aiki na zamani tare da samar da kwararrun ma’aikata masu mu’amala da abokan huldarmu yadda ya kamata.

Ya kara da cewa, wannan nasarar yana nuna cewa, aiki tukuru na da rabarsa kamar yadda muka tsayu a tsawon shekara uku. Babban burinmu shi ne abokan huldarmu, muna kuma kokarin gamsar da su ta hanyar amfani da dukkan kokarinmu don bayyana wa duniya cewa sune a gabanmu, mun dauki hanyar gudanar da harkokin banki ba tare da ruwa ba.

A takaitaccen jawabinsa, daya daga cikin wanda suka kirkiro da bankin, Mista Sherif Idi, ya danganta nasarar da suka samu ga masu hannun jari da abokan huldar bankin, ya kuma kara da cewa, “Muna godiya ga abokan huldar mu da masu hannun jarinmu wadanda sune suke zaburar da mu a nasarar da muke samu zuwa yanzu.

“Ina mai tabbatar muku da cewa, hukumar gudanarwa TAJBank da ma’aikatanta za su ci gaba da kare bukatun ku a dukkan harkokin bankin saboda yadda muka muhimmantar da ku”, in ji shi.

Taj
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Kotu Ta Kori Ƙarar Da APC Ta Shigar Kan Dakatar Da Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomin Kano
Tattalin Arziki

Kano Ta Tara Harajin Naira Biliyan 102 A Shekarar 2025, Ta Zama Jiha Ta Farko A Arewa

October 16, 2026
Samar Da Kayayyakin Cikin Gida Na Da Muhimmanci Wajen Ƙarfafa Tattalin Arziki – Dangote
Tattalin Arziki

Samar Da Kayayyakin Cikin Gida Na Da Muhimmanci Wajen Ƙarfafa Tattalin Arziki – Dangote

October 11, 2026
NPA Za Ta Ƙirƙiro Da Tsarin Kamun Kifi A Tashoshin Jiragen Ruwa – Ɗantsoho
Tattalin Arziki

NPA Za Ta Ƙirƙiro Da Tsarin Kamun Kifi A Tashoshin Jiragen Ruwa – Ɗantsoho

October 11, 2026
Next Post
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kama Hanyar Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba A Yankin Tsaunin Himalaya

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kama Hanyar Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba A Yankin Tsaunin Himalaya

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.