Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yau Litinin.
Da yake tsokaci game da ziyarar aiki da ministan wajen kasar Wang Yi ya kai wasu kasashen Afirka 4 a kwanan nan, Guo Jiakun ya ce, ziyarar ministan ta wannan karo ita ce ziyarar farko da ministan wajen Sin ya kai nahiyar Afirka bayan da aka daga dangantakar Sin da Afirka zuwa mataki na dukkan fannoni.
Najeriya Da Sin Abokai Ne Dake Haifarwa Juna Da Alfanu
Haka nan ya ce, wannan ziyarar ta nuna aniyar Sin da Afirka wajen tinkarar sauye-sauyen da ake samu a duniya cikin wannan karnin. Kuma tabbas, alakar Sin da Afirka za ta zama abin koyi ta fuskar gina al’umma mai makomar bai daya ta daukacin bil’adama.
Game da taron tattaunawa kan tattalin arziki da hada-hadar kudi tsakanin Sin da Birtaniya karo na 11 da aka gudanar kwanan nan kuwa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin da Birtaniya sun cimma sakamako guda 69 da suka shafi moriyar juna a lokacin taron.
Haka nan, bangarorin biyu sun yi imanin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Birtaniya na da alfanu ga ci gaban kasashen biyu, kuma za su ci gaba da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a sashen ayyukan samar da kayayyaki a duniya.
Game da yadda Amurka ta sanya wasu kamfanonin Sin cikin jerin sunayen wadanda za a sanya musu takunkumi kuwa, Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin tana adawa da gamin-gambizar da Amurka ke yi a kan manufar tsaron kasa, da yin katsalandan tare da takaita mu’amalar tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata.(Safiyah Ma)