Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Gombe, ta bayyana cewa an samu qaruwar sabin masu yin tazarar haihuwa a jihar, da kimanin mutane 28,561 daga watan Janairu zuwa Maris xin 2023.
Ko-odinetar sashin tazarar haihuwa a hukumar Grace Mabudi ce ta bayyana hakan yayin taron rubu’i na biyu na qungiyar Æ´an jarida masu aiki da qungiyar The Challenge Initiative (TCI) kan tazarar haihuwa a jihar.
- Gwamnan Gombe Ya Nada Njodi Sakataren Gwamnati, Misilli Daraktan Yada Labarai
- Rukuni Na 3 Na Alhazan Gombe Zasu Tashi Zuwa Madina A Yau Juma’a
Grace ta ce “Qaruwar bata rasa nasaba da jajircewar da kafofin watsa labarai da qungiyoyin ci gaba suke yi wajen wayar da kan jama’a musamman iyalai kan mahimmancin tazarar haihuwa. Gaskiya kuna qoÆ™ari”.
Sai dai ta yi qira ga ’ya’yan qungiyar su qara himma wajen qiran a qara samar da kayan da ake amfani da su wajen gudanar da wassu hanyoyin na tazarar haihuwa, wanda shi ne babban qalubalen dake fuskantar ayyukan tazarar a jihar.
A cewarta, jihar tana da wadatatun magungunan tazara, amma tana fama da qarancin kayan da ake amfani da su kamar su auduga, da sirinji, da safar hannu, filasta da sauransu, tana mai tabbatar da cewa dole sai da kayayyakin kafin a iya gudanar da wasu nau’o’in na tazarar haihuwa.
Tace “qarancin kayayyakin ya sanya ma’aikatan lafiya suna karvar wassu yan kuxaxe daga masu zuwa tazarar É—in sayar musu nasu da suka tanadar”.
Don haka ko’odinetar ta yi qira ga kungiyoyi masu bada gudunmawa da abokan hulxar ci gaba su qara samar da kayayyakin, lamarin da tace zai qara qarfafa gwiwar mata su riqa yin tazarar ta haihuwa a jihar.
Ko’odinetar wacce ta samu wakilcin mataimakiyar ta Mrs Aise Fada, ta ce asibitoci 456 ne ke yin ayyukan na tazarar haihuwa a faxin jihar.
Ko’odinetar ta ce wata qungiya mai fafutukar bunqasa lafiyar iyali za ta ziyarci jihar don gabatar da wata sabuwar hanyar tazarar haihuwa inda mace zata yiwa kanta allurar tazarar.
Ta ce za a koyawa mata yadda ake yin allurar, don su riqa yinta da kansu.
Grace Mabudi ta ce qungiyar zata horar da manyan jami’ai da masu sa kai na cikin al’umma, waxanda zasu ci gaba da ilimantar da sauran jama’a tare da koya wa mata yadda ake amfani da sabuwar dabarar.
Da take bayyana cewa sabon tsarin kyauta ne, Grace ta ce “Allurar ba ta da wani illa kuma kowane yi xaya yana aiki ne na tsawon watanni uku”.
Taron na rubu’i-rubu’i na tawagar yan jaridan, wanda qungiyar ta The Challenge Initiative ke tallafawa, yana nazari kan ayyukan baya da aka gudanar, da tsara sabbin dabaru kan yadda za a bunqasa tazarar a tsakanin matan jihar.
A nata jawabin, shugabar qungiyar yan jaridan Rabecca Caleb Maina, ta qarfafawa ‘yan qungiyar gwiwa kan su maida hankali kan bada labaran da suka shafi rayuwar al’umma a cikin rahotanninsu na tazarar haihuwa, waxanda zusu jawo hankulan jama’a da kuma bunqasa tazarar a jihar.
Rabecca ta kuma shawarci mambobin qungiyar kan qarin rahotanni daga asibitoci masu zaman kansu, savanin yadda ake yawan maida hankali kan asibitocin gwamnati.
Da take gabatar da wasu ayyukan qungiyar na rubu’i na biyu da suka haxa da rahotanni da labarai da sharhi da wallafe-wallafen da aka yayata kan tazarar haihuwa, shugabar ta ba da tabbacin jajircewar qungiyar wajen qara wayar da kan al’ummar jihar.