Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jihar Gombe ta fitar da kashi na uku na jerin sunayen maniyyata 554 a shirye-shiryen tashin su zuwa Madina yau.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar Muhammad D Muhammad, ya shaidawa LEADERSHIP Hausa cewa, fitar da jerin sunayen biyo bayan nasarar jigilar rukuni na biyu na maniyyatan jihar 560 ne jiya Alhamis zuwa ƙasa mai tsarki.
- Hajjin Bana: Adadin Alhazan Nijeriya A Saudiyya A Yanzun Ya kai 24,324
- NAHCON Ta Nemi Alhazai Su Biya Kashi 40 Na Dala 250 Na Jigilarsu
Jihar ta yi sawun farko na maniyyata 560 ne a ranar Laraba, waɗanda suka haɗa da maza 350, mata 205 da jami’ai biyar ta kamfanin jiragen sama na Max Air.
Yayin jawabinsa na bankwana ga maniyyatan jihar a ranar Talata, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya buƙace su da su kasance jakadu nagari ga jihar da Nijeriya, tare da yi wa Gombe da ƙasar addu’o’i don samun ɗaukin Allah game da matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ake ciki.
Jihar Gombe dai tana da adadin maniyyata 2556 da za su sauƙe farali a aikin Hajjin na bana.