Mutane da dama, galibinsu ƙananan yara, sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya afku yayin bikin nuna al’adun ƙarshen shekara da aka shirya wa yara a makarantar Basorun High School da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Duk da cewa ba a bayyana yawan adadin mutanen da suka mutu ba, gwamnatin jihar ta tabbatar cewa mafi yawan waɗanda suka rasa rayukansu ƙananan yara ne.
- Manufar Sin Ta Yada Zango Ba Tare Da Biza Ba Ta Kara Jawo Hankalin Masu Yawon Shakatawa Na Ketare
- Da Dumi-Dumi: An Yi Kutse A Shafin Hukumar Kididdiga Ta Kasa
Turmutsutsun ya faru ne a ranar Laraba, inda wasu kuma suka samu raunuka da ke buƙatar kulawar gaggawa.
An kai waɗanda lamarin ya shafa zuwa asibitoci mafi kusa a Ibadan domin kula da su.
A wata sanarwa da Prince Dotun Oyelade, kwamishinan yaɗa labaran jihar, ya fitar, ya bayyana cewa ba su da masaniya kan taron kafin afkuwar lamarin.
Ya kuma ce da sun bayar da goyon baya don tabbatar da tsaron taron da aka shirya wa yara.