Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya naɗa sabbin shugabannin riƙo a ƙananan hukumomi 23 na Jihar Ribas, duk da umarnin kotu da ya hana shi yin hakan.
Tun da farko, Kotun Tarayya da ke Fatakwal ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Adamu Tukaki Muhammed, ta bayar da umarni cewa Ibas ba zai naɗa shugabanni ba har sai an yanke hukunci a kan wata ƙara da ke gabanta.
- Kotu Ta Daure Ango Kan Liƙi Da Kuɗi A Wajen Bikinsa A Kano
- Ribadu Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Daina Biyan ‘Yan Bindiga Kuɗin Fansa
Sai dai da safiyar ranar Laraba, gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa Ibas ya amince da naɗin sabbin shugabannin ƙananan hukumomi.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibiba Worika, ya sa wa hannu, ta kuma bayyana cewa an kuma dawo da wasu hukumomi da kwamitoci da aka dakatar a baya.
Sanarwar ta ce duk waɗannan naɗe-naɗen za su fara aiki daga Litinin, 7 ga watan Afrilu, 2025.
A ranar 28 ga watan Maris, 2025, wata ƙungiya mai kare haƙƙin jama’a da ake kira Plex Centre for Civic Education Initiative ta shigar da ƙara a kotu, tana neman kotu ta dakatar da naɗin shugabannin ƙananan hukumomin jihar.
Alƙalin ya yarda da buƙatar ƙungiyar, inda ya bayar da umarnin wucin-gadi, sannan ya ɗage sauraren shari’ar zuwa 14 ga watan Afrilu, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp