Hukumar ICPC ta samu gurfanar da Mohammed Idris, wani jami’i a ƙofar shigen shiga wurin Hajji da ɗiban kaya na filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagas, kan laifin bayar da bayanan ƙarya da kuma cin da kuɗaɗen haram.
A gaban Mai shari’a O.A. Fadipe na kotun laifuka ta musamman da ke Ikeja, lauyan ICPC, Yvonne Williams-Mbata, ta gabatar da shaida kan yadda bincike ya gano ɓacewar kuɗi har Naira miliyan goma sha ɗaya da dubu ɗari biyu da talatin da huɗu (N11,234,000) a ƙarƙashin kulawar wanda ake tuhuma daga watan Fabrairu 2001 zuwa Afrilu 2021.
- Yadda Tayar Jirgin Saman Max Air Ta Kama Da Wuta Yayin Sauka A Kano
- Fashewar Tayar Jirgi A Kano: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kamfanin Max Air Na Tsawon Watanni Uku
Mai shari’a Fadipe ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin ɗaurin shekara guda kan kowanne daga cikin tuhumce-tuhumcen biyu, ko kuma ya biya tarar Naira miliyan ɗaya. Hukuncin zai gudana tare na farko. Haka kuma, an buƙaci ya shiga yarjejeniya da kotu da adadin Naira miliyan biyu (N2,000,000), inda rashin cika sharuɗɗan zai kai shi ga ɗaukar hukuncin ɗaurin shekaru goma.