Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka (ICPC), ta ce za ta binciki wasu korafe-korafe da aka gabatar kan jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) dangane da zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Edo.
Idan za a iya tunawa, hukumar zabe ta bayyana Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 21 ga watan Satumba, 2014 a Jihar Edo.
- Rikicin PDP: A Daina Maganar Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2027, A Maida Hankali Kan Jam’iyya –Saraki
- An Kafa Kawancen Hadin Gwiwar Taron Masanan “Global South”
Mai magana da yawun hukumar ICPC, Demola Bakare, ya tabbatar da cewa an samu wasu koke a kan wasu jami’an hukumar zabe kan almundahana.
Wasu rahotanni sun bayyana yadda masu sa ido kan zaben jihar a makon da ya gabata suka mamaye hedikwatar hukumar ICPC inda suka shigar da kara kan INEC.
Masu sa idon wadanda akasarinsu lauyoyi ne karkashin inuwar ‘Tap Initiatibe’, sun bukaci da a kama jami’an hukumar tare da gurfanar da su a gaban kuliya bisa zargin buga takardar sakamako zabe guda biyu (EC8A).
Sai dai mai magana da yawun hukumar ta ICPC ya shaida cewa, “A duk lokacin da muke yin wani bincike ba za mu bayyana shi a fili ba har sai mun kammala.
“Kuna iya tabbatar da cewa an karbi koken, ana sane da shi. Tabbas, idan akwai wani abu a cikinsa, za mu yi wani abu game da shi.
“Amma ba al’adarmu ba ce mu gaya wa kowa abin da muke yi. Mun karbi takardar koke kuma muna sane da su. Za mu tabbatar da cewa za a yi wani abu a kai.”