Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya koka ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan karuwar harkokin ta’addanci a Jihar Zamfara, yana mai cewa, in har aka samu nasarar fattakar ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara tamkar an kore su ne daga yankin arewa gaba daya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata. Ya kuma kara da cewa, barin ‘yan ta’adda na cin karensu babu babbaka a yankin Zamfara yankin arewa gaba daya zai ci gaba da kasancewa a cikin hadari.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Da Takwaransa Na Kasar Kazakhstan Sun Mika Sakwannin Murnar Kaddamar Da “Shekarar Yawon Bude Ido Ta Kazakhstan” A Sin
- Gwamna Dauda Lawal Ya Gana Da Ministan Ruwa Domin Kammala Ayyukan Ruwa A Zamfara
Daga na Gwamna Lawal ya kuma ce, “A yau a mastayina na Gwamnan Jihar Zamfara na zo fadar shugaban kasa (villa) inda na gana da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu domin na yi masa bayanin irin matsalolin da muke fuskanta na rashin tsaro a Jihar Zamfara, wanda kuma tattunawar tamu ta yi amfani kwarai da gaske, domin ya bani tabbacin cewa, da ikon Allah zai yi duk abin da zai yi ya taimaka mana a Jihar Zamfara don mu samu sauki. Saboda idan ka duba yanzu duk matsalolin tsaro da ake samu yanzu a kusa yankin arewa gaba daya abubuwa ne da suke tasowa daga Zamfara, saboda haka idan aka yi abin da ya kamata a yankin Zamfara kusan dukka yankin arewa za a samu sauki”
Ya kuma bayyana cewa. “Na ji dadin wannan tattauanwar na kuma yi farin ciki sosai. Haka kuma ya gamsu da dukkan bayanin da na yi masa a ka matsalolin da muke fuskanta a Zamfara na mastalar tsaro. Wasu matsalolin da na yi masa bayani a kai da can bai san dasu ba, amma yau ya san kusan komai da ke faruwa a wannan jihar ta mu”.
Tun da ya dare karagar mulkin jihar ne, Gwamna Lawal yake fadi tashin ganin an samu zaman lafiya a jihar Zamfara. Cikin matakan da ya dauka akwai da kafa rundunar Askarawan Zamfara wanda aka shirya za su yi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro don fatattakar ‘yan bindiga.
A kwanan nan ma ya ziyarci shugaban rundunar tsaro Janar CG Musa inda ya nemi a kara yawan sojojin da ke aiki a Zamfara don dakile ayyukan ‘yan ta’adda.