Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan da kada ya sake ya fito takarar shugabancin ƙasa a 2027.
A cewar Shehu Sani, idan Jonathan ya amince ya tsaya takara, zai iya rasa mutuncin da yake da shi a Nijeriya da ma ƙasashen waje.
- Amurka Ta Yaba Da Nasarar Nijeriya Wajen Kama Shugabannin Ansaru
- PDP Ta Yi Fatali Da Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi Na Okura, Ta Nemi A Soke
Ya ce a baya, musamman a zaɓukan 2019 da 2023, an yi ƙoƙarin tursasa wa Jonathan ya tsaya takara, amma ya ƙi saboda ya san hatsarin da hakan zai iya jawo masa wajen kare martabarsa.
Shehu Sani ya ƙara da cewa jam’iyyar PDP da ta kawo Jonathan mulki a baya ba ita ce irin wadda ya sani ba a yanzu, saboda rikice-rikice da rabuwar kawuna sun yi mata yawa.
“Yanzu PDP ta yi rauni sosai, hatta wasu ‘yan majalisa da gwamnoninta sun koma APC. A ganinmu Jonathan ya fi dacewa ya ci gaba da zama shugaba da ake daraja shi a gida da waje, ba tare da sake tsayawa takara ba,” in ji shi.
Ya kuma yi nuni da cewa ko da PDP na son amfani da Jonathan don ta dawo da ƙarfinta, ba zai yiwu ya warware matsalolin da jam’iyyar ke ciki shi kaɗai ba.
Dangane da ra’ayin da wasu ke yi. A cewa Jonathan na iya kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu idan ya tsaya takara, Shehu Sani ya ce ba ya ganin hakan zai yiwu.
“Jonathan ya riga ya yi nasa lokacin, kuma mutane suna girmama shi a yanzu. Abin da ya rage masa shi ne ya kiyaye wannan daraja, kar ya ɓata ta, ta hanyar sake tsayawa takara,” a cewarsa.
Jonathan dai ya daina shiga harkokin siyasa tun bayan da ya faɗi zaɓe a hannun tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a 2015, amma PDP ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da shi kan yiwuwar ya tsaya mata takara a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp