Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa idan har ‘yan Nigeria suka zabe shi ya zama shugaban kasa zai kawo karshen yajin aikin malaman Jami’a (ASUU).
Tsohon Ministan tsaron ya bayyana hakan ne a wata hirar ta musamman da manema labarai a Gombe.
Ya ce zai baiwa bangaren ilimi fifiko domin duk wanda ya san Kano lokacin yana gwamna ya san ya bar tarihi a jihar wajen inganta fannin.
A cewarsa, ba burinsa bane kwashe kudin Nijeriya don biya wa wasu bukata.
Sannan ya kuma ce ba zai kwashe kudin kasa ba, kuma ba zai bari a kwashe ba dole sai da dalilin abin da za a yi da kudin.
Wasu daga cikin dalilan da suka sanya al’ummar jihar Kano suke goyon bayan gwamnan dai sun hada da kai daliban jihar makarantun kasashen waje domin yin karatu.