A bana ne, shawarar Ziri daya da hanya daya, shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013 take cika shekaru 10 cif da kafuwa. Da farko dai shawarar ta mayar da hankali ne kan batun zuba jari a fannin ababen more rayuwa, da Ilimi, da gine-gine, da hanyoyin mota da layin dogo, da rukunin gidajen kwana, da tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da dan-Adam ke bukata a al’amuran rayuwar yau da kullum.
Alkaluma na nuna cewa, shawarar Ziri daya da hanya daya ta kasance tsarin da ya gudanar da ayyukan more rayuwa da zuba jari mafi girma a tarihi, inda ya shafi sama da kasashe 68, ciki har da kaso 65 cikin 100 na yawan al’ummar duniya, da kaso 40 cikin 100 na ci gaban GDPn duniya a shekarar 2017.
Shawarar Ziri daya da hanya daya, ta yi nasarar magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arziki a yankin Asiya da fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai. Masana sun yi imanin cewa, shawarar tana da muhimmanci sosai wajen bunkasa alakar kasa da kasa.
Bugu da kari, shawarar, ta baiwa kasar Sin damar raba dabarun ci gaban ta da sauran kasashen Afirka masu tasowa, wanda hakan ya haifar da nasarar kammala layukan dogo, da titunan mota, da tashoshin jiragen ruwa da na sama, a birane da garuruwa a sassa daban-daban na kasashen Afirka da Asiya da ma sassan duniya, ayyukan da suke taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar irin wadannan kasashe. Kuma sabanin yadda kasashen yamma ke zargi da ma neman bata sunanta, idan aka dubi ci gaban da nahiyar Afirka ke samu a fannin samar da ababen more rayuwa, za a fahimci irin taimako da shawarar take baiwa nahiyar. Hakika kasar Sin na samar da agaji irin wanda kasashen Afirka ke bukata.
Tun bayan da aka gabatar da shawarar, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta yi aiki tare da kasashen da abin ya shafa, wajen zurfafa hadin gwiwar moriyar juna bisa ka’idar yin shawarwari mai zurfi, da ba da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna, kana ta cimma nasarori masu tarin yawa. Bayanai sun nuna cewa, kasar Sin tana kokarin gina layukan dogo a kasashen nahiyar Asiya, da Turai, da arewacin Amurka, da kuma Afirka, wadanda suka zama shaidun aikin raya shawarar Ziri daya da hanya daya da kuma hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. Babu shakka, shawarar Ziri daya da hanya daya, ta zama wani babban dandalin hadin gwiwa na kasa da kasa mafi girma a duniya. Idan rana ta fito, tafin hannu ba ya rufe ta. (Ibrahim Yaya)