ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Idan Rana Ta Fito…

by yahuzajere
3 years ago
rana

A bana ne, shawarar Ziri daya da hanya daya, shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013 take cika shekaru 10 cif da kafuwa. Da farko dai shawarar ta mayar da hankali ne kan batun zuba jari a fannin ababen more rayuwa, da Ilimi, da gine-gine, da hanyoyin mota da layin dogo, da rukunin gidajen kwana, da tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da dan-Adam ke bukata a al’amuran rayuwar yau da kullum.

Alkaluma na nuna cewa, shawarar Ziri daya da hanya daya ta kasance tsarin da ya gudanar da ayyukan more rayuwa da zuba jari mafi girma a tarihi, inda ya shafi sama da kasashe 68, ciki har da kaso 65 cikin 100 na yawan al’ummar duniya, da kaso 40 cikin 100 na ci gaban GDPn duniya a shekarar 2017.

  • Angola Ta Yabawa Ingancin Sabon Filin Jirgin Sama Da Kamfanin Sin Ke Ginawa A Kasar

Shawarar Ziri daya da hanya daya, ta yi nasarar magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arziki a yankin Asiya da fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai. Masana sun yi imanin cewa, shawarar tana da muhimmanci sosai wajen bunkasa alakar kasa da kasa.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari, shawarar, ta baiwa kasar Sin damar raba dabarun ci gaban ta da sauran kasashen Afirka masu tasowa, wanda hakan ya haifar da nasarar kammala layukan dogo, da titunan mota, da tashoshin jiragen ruwa da na sama, a birane da garuruwa a sassa daban-daban na kasashen Afirka da Asiya da ma sassan duniya, ayyukan da suke taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar irin wadannan kasashe. Kuma sabanin yadda kasashen yamma ke zargi da ma neman bata sunanta, idan aka dubi ci gaban da nahiyar Afirka ke samu a fannin samar da ababen more rayuwa, za a fahimci irin taimako da shawarar take baiwa nahiyar. Hakika kasar Sin na samar da agaji irin wanda kasashen Afirka ke bukata.

Tun bayan da aka gabatar da shawarar, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta yi aiki tare da kasashen da abin ya shafa, wajen zurfafa hadin gwiwar moriyar juna bisa ka’idar yin shawarwari mai zurfi, da ba da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna, kana ta cimma nasarori masu tarin yawa. Bayanai sun nuna cewa, kasar Sin tana kokarin gina layukan dogo a kasashen nahiyar Asiya, da Turai, da arewacin Amurka, da kuma Afirka, wadanda suka zama shaidun aikin raya shawarar Ziri daya da hanya daya da kuma hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni.  Babu shakka, shawarar Ziri daya da hanya daya, ta zama wani babban dandalin hadin gwiwa na kasa da kasa mafi girma a duniya. Idan rana ta fito, tafin hannu ba ya rufe ta. (Ibrahim Yaya)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

rana
yahuzajere
+ postsBio
  • yahuzajere
    Da Kujerar Mulki Gara Zaman Lafiyar Kano
  • yahuzajere
    Ya Kamata Amurka Ta San Ana Barin Halal Don Kunya
  • yahuzajere
    Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano
  • yahuzajere
    Sin Ta Kaddamar Da Gagarumin Bikin Ba Da Lambobin Yabo Na Kasar Sin

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Cote d’Ivoire

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Cote d’Ivoire

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.