Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa kusan duka masu aikata laifukan garkuwa da kashe-kashe a Kudu Maso Gabas ƴan ƙabilar Igbo ne, ba Fulani makiyaya kamar yadda ake yawan zargi ba. Ya ce wannan ya fito fili ne daga binciken hukumomin tsaro tun bayan hawansa mulki kimanin shekaru uku da suka wuce.
Soludo ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ƴan asalin jihar da ke zaune a ƙasashen waje a birnin Maryland, Amurka. A cewarsa, “99.99% na waɗanda aka kama da hannu a aikata laifuka a jihar Igbos ne.” Ya ƙalubalanci tunanin cewa Fulani ne ke haddasa fitintinu, yana mai cewa ƴan gida ne ke ba da mafaka da abinci ga waɗannan miyagun a dazuka.
- Tinubu Ya Kai Ziyarar Aiki Jihar Anambra
- Gwamnan Anambra Ya Amince Da Biyan Mafi Karancin Albashi Na Naira 70,000
Gwamnan ya jaddada cewa yawancin masu iƙirarin ƴan gwagwarmaya ne kawai ke ɓoye a ƙarƙashin wata siyasa don aikata laifuka. Ya ce idan har za a kawo zaman lafiya da cigaba a yankin, dole ne a fuskanci gaskiyar halin da ake ciki da kuma yarda cewa matsalar gida ce.
A ƙarshe, ya yi kira ga ƴan ƙasashen waje su tallafa da zuba jari a jiharsu ta asali tare da ɗaukar nauyin ci gabanta. Ya ce kowa na da rawar da zai taka wajen samar da tsaro da bunƙasar jihar Anambra da Kudu Maso Gabas gaba ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp