Katafaren kamfanin fasaha na kasar Sin Huawei, ya kaddamar da gasar fasahar sadarwa ta zamani (ICT) ta shekarar 2025 zuwa 2026 a duk fadin kasar Uganda, domin bunkasa hazaka a kasar.
A matsayinsu na manyan gobe, samun ilimin fasaha a tsakanin matasa na da muhimmanci gaya wajen raya kasashe. Sabanin yadda a ko da yaushe kasashen Afrika ke zama koma baya a duk wani sabon abu da ya bullo a duniya, yanzu batun ya sauya sakamakon yadda hadin gwiwarsu ke kara zurfi da fadada da kasar Sin. Mun san cewa, hadin gwiwar kasashen Afrika da Sin na gaba-gaba wajen bayar da gudunmuwar ga habakar tattalin arziki da kyautatuwar rayuwa da ma baki dayan ci gaban da nahiyar ke samu a shekarun baya bayan nan.
Har kullum na kan bayyana duk wani ci gaba da Sin ta samu a matsayin ci gaba ga kasashen Afrika. Ba kadai ga Uganda ba, ana gabatar da makamancin shirin a kasashe da dama na Afrika ciki har da Nijeriya. Misali, yayin taron kolin Beijing na FOCAC a bara, kamfanin Huawei ya ce zai kaddamar da shirin ajin tafi-da-gidanka na Digitruck a Nijeriya, domin horar da ilimin fasahar zamani ga dalibai 3,000 a kowacce shekara. Wannan tallafi ya kara habakawa tare da ba kasar damar cimma burinta na bayar da horon fasahar ga matasa miliyan 3 zuwa 2027, domin su zamo masu dogaro da kai.
A matsayinta na mai jagorantar zamanantar da duniya, Sin tana gabatar da ilimin da ya danganci fasahar zamani ga kasashen Afrika domin su tsaya da kafarsu tare da samun kyakkyawar makoma. Wannan zai samarwa matasa dama mara iyaka ta fadada ilimi da fahimta da samun aikin yi da zai kai su ga yin kirkire kirkiren da za su tallafawa al’ummar da cike gibin dake akwai tsakanin masu ilimi da marasa shi. Kuma yayin da duniya ta dunkule wuri guda saboda fasahohin zamani, matasa a nahiyar Afrika za su kara fahimtar yanayin da duniya take cike da fahimtar juna da kara wa juna sani tsakaninsu da takwarorinsu na kasashen waje, lamarin da zai share fagen gogayyar ilimi da samar da ci gaban kasashe da duniya baki daya. Hakika wannan yunkuri na kamfanin Huawei na Sin yana daukaka burin Sin na gina al’ummar Sin da Afrika da ma duniya, mai kyayyawar makoma ga daukacin bil adama. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp