ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 19, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Illar Amfani Da Manhajar VPN Ta Kyauta

by Ibrahim Sabo
4 years ago
VPN

Manhajar Free VPN, wani application ne da yake ba da damar yin dukkan nau’i na browsing a kyauta, amma yana da illoli matuka ga wayoyi da kuma rashin sirri ga mutum.

Yin amfani da manhajar VPN na kyauta yana da matukar hadari, zai iya iya janyo wa mutum abin da ko da wasa baya taba tunaninsa.

  • Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Sin Ta Fadada Samar Da Kwayoyin Ibuprofen Da Paracetamol 

Gara ma wanda ake biya kafin amfani da su din, domin shi din ana iya kare bayanan sirri na mai amfani da shi a kan kudin da bai taka kara ya karya ba.

ADVERTISEMENT

Akwai mutane da dama wadanda suke jin dadin amfani da manhajar BPN na kyauta, to ya kamata tun wuri su sani cewa, amfani da BPN yana tattare da illoli, gasu a kasa za mu yi bayani daya bayan daya.

Za A Iya Satar Bayananka

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

Yawancin masu amfani da BPN ba su da masaniyar za a iya satar bayanansu cikin sauki. Daya daga cikin muhimman dalilan amfani da manhajar BPN shi ne ganin an kare ka daga masu kutse, to amma fargabar ita ce maganar gaskiya wasu manhajojin na BPN na kunshe da wani siddabaru da ake amfani da shi wajen satar bayananka da kuma amfani da wannan dama wajan aiwatar da wata mummunar manufa da ake son cimmawa.

Irin wadannan manhajoji na kyauta na BPN na amfani da tallukan da suke sanya wa masu amfani da su wajan wawashe bayanansu, kasancewar sun dogara ne da ‘yan tallukan da suke samu wajen samun kudin shiga.

Bibiyar Duk Abin Da Kake Yi

Wasu suna amfani da Manhajar BPN ne, saboda kare sirrinsu a lokacin da suke bincike a Internet ba, to sai dai yawancin manhajojin BPN na kyauta na da wasu mutane da aka sanya da ke bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikinsu, suna tattara bayanan masu amfani da su, don haka a wannan bigire maimakon a aiko maka da wani tsari da kake da damar amincewa da shi ko ka latsa kalmar a’a, sai kawai a tunkudo maka talla, wanda a lokacin da kake kallonsa sai kuma a rika kwasar bayananka salin alin ba tare da ka danna komai ba.

Takaita Samun Bayanai

Yawancin BPN na kyauta na takaita adadin bayanan da za ka iya amfani da su. Suna yin wannan ne don tura masu amfani da su zuwa tsarin da ake biyan kudi kafin a samu cikakkiyar damar yin abinda ake son a yi, kamar yadda Hausawa ke cewa ”Iya kudinka iya shagalinka”

Manhajar BPN na haifar da damuwa ga masu amfani da ita saboda yadda take jinkirta sadarwar Internet (rashin sauri).

Manhajar BPN na kyauta na haifar da jinkiri wajen samun bayanai a Internet, abin da ke kawo damuwa ga wanda ke amfani da su, to dalilin shi ne yawancin mutane na raja’a ne ga na kyauta don cin bulus.

Sannan su kansu tallukan da suke sanya wa da zummar satar bayanai na iya haifar da rashin saurin na Internet, dalilin sanya tallan shi ne tun da masu amfani da su garabasa kawai suke ci, to bari su tallata wata haja tun da dama masu karin magana sun ce ”Da ruwan ciki ake jan na Rijiya”.

Barazanar Harbuwa Da Cututtukan Intanet

Manhajojin da ake amfani da su wajen sadarwa a waya ko na’urar kwamfuta ko kuma Internet na dauke da wasu hanyoyi da yawa da ake sanya wa a cikinsu wajen satar bayanai ko yin kutse ko shirya wani siddabaru.

Wasu manhajojin na BPN da ake amfani da su a kyauta ana tsara su ne da zummar cewa masu su suna da ikon sarrafa bayanan mutane yadda suka ga dama, kuma suna ba da wannan ikon ga abokan cinikinsu masu biyan kudi don riba.

Wannan yana da matukar hadari kamar yadda ma su aikata laifuka ta yanar gizo ke iya yin amfani da wannan yanayin don kaddamar da hare-hare kan masu amfani da BPN da ba su da masaniyar duk wannan al’amari.

Manhajojin BPN na tattare da sarkakiya iri iri da ke da bukatar zuba kudi da yawa a harkar don samar da kariya da kuma tsare bayanan ma su amfani da su. Akwai kuma bukatar masu su, su rika sabunta tsare tsaren ba da kariyar da suke amfani da su akai-akai daidai da zamani domin tabbatar da kare abokan huldarsu.

Sai dai kash, rashin mayar da hankali ga wadannan abubuwa da suka kamata ne ya sa masu manhajar BPN ta kyauta ke cin karensu babu babbaka ta hanyar cusa talluka da wasu tsare-tsare da ke zama babban hadari ga masu amfani da manhajar.

A kashin gaskiya, wannan ba wai kawai abu ne mai matukar hadari ba, ya kuma ci karo da dokokin bayar da kariya da tsaro da su kansu ka’idojin amfani da manhajojin na BPN.

Amfani da manhajar BPN zai zama ba ka da cikakkiyar kariya a dukkan mu’amalarka ta Intanet. Wasu kasashen tuni sun haramta amfani da manhajar BPN, saboda hadarin dake tattare da ita. Dukkan sirrikanka suna hanun BPN muddin kana amfani da manhajar BPN. Sannan amfani da manhajar BPN yana zukar data fiye da na normal data.

VPN
Ibrahim Sabo
+ postsBio
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (II)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (I)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Mene Ne Tsarin 5G?
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Yadda Ake Sarrafa Rubutu Ta Word-Processing

MASU ALAKA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
Rahotonni

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Rahotonni

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Next Post
An Kama Saurayin Da Ake Zargi Da Kashe Budurwarsa

An Kama Saurayin Da Ake Zargi Da Kashe Budurwarsa

LABARAI MASU NASABA

Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Bauchi Ta Yi Allah-wadai Da Kama Masu Kaɗa Ƙuri’a

Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Bauchi Ta Yi Allah-wadai Da Kama Masu Kaɗa Ƙuri’a

September 19, 2026
Rikicin Fili: Harsashi Ya Yi Ajalin Ɗalibin Jami’a A Neja

Rikicin Fili: Harsashi Ya Yi Ajalin Ɗalibin Jami’a A Neja

September 19, 2026
Motoci Masu Amfani Da CNG Da Lantarki Sun Rage Kuɗin Sufuri Da Kashi 83 – Tinubu

Motoci Masu Amfani Da CNG Da Lantarki Sun Rage Kuɗin Sufuri Da Kashi 83 – Tinubu

September 19, 2026
Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Angola: Kasar Sin Tana Da Shugaba Mai Hangen Nesa

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Angola: Kasar Sin Tana Da Shugaba Mai Hangen Nesa

September 19, 2026
2027: Magoyin Bayan Atiku Ya Fice Daga ADC, Ya Goyi Bayan Tinubu

2027: Magoyin Bayan Atiku Ya Fice Daga ADC, Ya Goyi Bayan Tinubu

September 19, 2026
Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato

Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato

September 19, 2026
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 12, Sun Ceto Mutane 66 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 12, Sun Ceto Mutane 66 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

September 19, 2026
An Dakatar Da Jami’an NSCDC 21 Kan Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

An Dakatar Da Jami’an NSCDC 21 Kan Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

September 19, 2026
Ku Rage Farashin Mai, Ku Sakarwa Ƴan Nijeriya Mara – Atiku Ga Tinubu

Ku Rage Farashin Mai, Ku Sakarwa Ƴan Nijeriya Mara – Atiku Ga Tinubu

September 19, 2026
Portugal Ta Gayyaci Ronaldo Gasar UEFA Nations League

Portugal Ta Gayyaci Ronaldo Gasar UEFA Nations League

September 19, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.