Mafi yawan lokaci, maza na amfani da matsattten dankamfai; domin kara suturta al’aurarsu tare da tsare al’aurar daga bayyanar surarta yayin da ta mike, musamman bayan sanya manyan tufafi kamar riga ko wando.
Sai dai a bangare guda, masana sun bayyana cewa; sanya wannan matsatttsen dankamfai, na da matukar illa ga lafiyar da namiji.
- Gwamnatin Kaduna Ta Mallaka Wa Rundujar Sojin Sama Fili Sama Da Hekta 43 Don Gina Gidaje
- Gwamnati Ta Samo Jarin Fiye Da Dala Biliyan 2 A Bangaren Wutar Lantarki
Abin da ya kamata a fahimta shi ne, a cikin ‘ya’yan maraina ake samar wa tare da adana maniyyi, wanda ya kunshi ‘ya’yan rai (Sperm cells) a turance. ‘Ya’yan rai su ne, kwaikwayen haihuwa na da namiji.
Har ila yau, daga cikin hikimar Allah (SWT), na saukar da jakar ‘ya’yan maraina kasa daga jiki; akwai samar da dumin kasa da dumin jiki. Wato ‘ya’yan maraina suna bukatar muhalli mai sanyi fiye da jiki, domin samar da lafiyayyun wadannan ‘ya’ya na rai.
Saboda haka, saukar da jakar ‘ya’yan maraina ta yi a kasan jiki, yana samar da raguwar dumi da maki 4 zuwa 6 na ma’aunin salshiyos kasa da dumin jiki, wanda hakan shi ne kyakkyawan yanayin da ‘ya’yan marainan za su iya samarwa tare da adana lafiyayyun ‘ya’yan rai.
Don haka, wajibi ne a lura domin sanya matsatttsen dankamfai zai iya daga jakar ‘ya’yan maraina tare da danfare ta ko takure ta da jiki. Sannan, hakan zai sa yanayin dumin ‘ya’yan marainan ya karu, ya kuma saje da na jiki.
Har ila yau, bincike ya nuna cewa; mazan da suke sa matsatttsen dankamfai tsawon rana, suna da karancin adadin ‘ya’yan rai idan aka kwatanta su da mazan da ba sa wa.
Bugu da kari. sanya matsatttsen dankamfai na takaita ko rage gudanar jini a al’aura da kuma lafiyar al’aurar da namiji.
Kazalika, ta bangaren tsafta sa matsatttsen dankamfai na haifar da gumi tare da rike danshi ga al’aura da kewayensa, idan ya jima ba a canja shi ba. Saboda haka, bukatar yawan canja shi akai-akai.
Amma babbar mafitar ita ce, kawai a nemi dankamfai mai yalwa (boder), wanda ba zai takure al’aurar ba, ma’ana a yi amfani da wanda za ta sakata ta wala.
Mun rubuto daga Turakar Dakta Maryam AA
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp