Kwanan nan ne dai shugaba Donald Trump na America ya fara aiwatar da alwashin da ya dauka, na kakaba haraji a kan kayayyakin da ake shigar da su cikin America daga kasashen waje, a matsayin wani yunkuri na farfado da irin wadannan masana’antu a America. Wannan mataki na rashin hangen nesa ya janyo Allah wadai daga kasashen duniya masu huldar cinikayya da America, domin kuwa mataki ne na rashin hankali.
Ba ma adawa da ganin America ta farfado da masana’antunta, to amma matakin da America ta dauka domin cimma wannan buri shi ne babban kuskurenta. Domin kuwa takurawa sauran kasashe, ba shi ne zai haifar mata da da mai Ido ba. Kakaba haraji a kan kayayyakin da ake shigar da su America ba zai amfani masana’antun America ba, domin kuwa Mr. Trump bai bi tsarin da ya dace ba, kuma girman kai ya hana shi neman shawarwari daga masana a fannin tattalin arzikin kasa ba.
- Sin: Matakin Harajin Kwastam Da Amurka Ta Dauka Babakere Ne
- Tsakanin Kafa Shingaye Da Gina Gada: Yadda Matakan Amurka Da Sin Suka Bambanta Sosai
A wannan gabar za mu iya cewa “Dara ta ci gida”. Domin kuwa wannan mataki ya janyo mummunar illa ga tattalin arzikin America ta fannoni da dama. Alal misali, farashin kayayyaki a America ya yi tashin gwauron zabo. Ke nan a nan zamu iya cewa haka ba ta cimma ruwa ba. Domin kuwa duk wannan haraji da Trump ya sanya, a karshe a kan Amerikawa zai kare.
Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu kansu biyo bayan maida martani da China tayi na ramuwar gayya. Domin kuwa sai da gwamnatin America ta kashe kimanin dala biliyan 30 wajen tallafawa manoman kasar kan asarar da suka tafka, biyo bayan harajin da China ta kakabawa wasu daga cikin amfanin gonar America da ake shigar da su China.
Sabo da haka a nan za mu iya bugun gaba mu ce “Kwalliya bata biya kudin sabulu ba” a kan matakin da shugaba Trump ya dauka na sanya haraji akan kayayyakin da ake shiga da su America daga China da sauran kasashen duniya.
Tabbas Mr. Trump ya fahimci babban kuskuren da ya tafka na daukar wannan mataki na rashin sanin ya kamata. Watakila yana jin kunyar ya fito ya fadawa duniya cewa ya janye wannan mataki, shi ya sanya ya fake da cewa ya jinkirta ci gaba da aiwatar da harajin har zuwa kwanaki 90, ko da yake ya ce ban da China. Babu makawa nan ba da jimawa ba shugaba Trump zai lashe aman da ya yi, musamman idan talakawan America suka gaza jimrewa matsatsin tattalin arziki sakamakon hauhawar farashin da rashin aikin yi da sakamakon wannan mataki da Trump ya dauka. (Lawal Mamuda)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp