Illa ta biyu wadda ba karamin tasiri take yi ba idan aka rasa samun rashin hadin kan Magidanta a Unguwa ko Gari inda kuma illa ce da zata haifar da wata kafa ce, yadda cutar sannu a hankali take samun kafar shiga a Unguwa ko kuma Gari.
Muddin aka wayi gari a samu Unguwa ko Gari basu damu da tsaftace muhalli ba maganar gaskiya ba karamar matsala za a shiga ba,musamman ace an samu barkewar annobar wata cuta.
- Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Max Air Ya Rasu
- Juriyar Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya
Idan ba kula da tsaftace muhalli ba,wannan ya hada daga cikin gida da waje,ya kuma kasance ko wanne Magidanci yana yin wannan dabi’ar data kamata.
Da zarar an ce Magidanta basu damu da shi al’amarin tsaftace muhalli ba, shikenan an kama hanyar gaiyatar nau’oin cututtuka daban- daban.
Sanin kowa ne kwayoyin cuta sun fi son wuraren da ba tsaftacesu don haka muddin dai akwai dauda ko kazanta a wuri ko shakka babu sai an samu su kwayoyin cutar.
Su ne ke kasancewa wata madafa da kwayoyin cuta suke bukata wajen samun damar karfi na yadda za su kara yaduwa, domin duk wuraren da dauda ko kazanta take, ba inda su kwayoyin cutar suke fi sha’awar kasancewa kamar cikin irin yanayin.
Alalmisali idan muka fara da cutar Amai da zawo ko Kwalara sanin kowa ne ba karamar kazanta bace wadda ta kai ta kawo, zata iya kasancewa sanadiyar kamuwa da ita.
Dama ita sau da yawa duk inda ake samun barkewarta wurare ne da mutane suka yi yawa, ya kasance ba a kulawa da tsaftace muhalli ba.Bama kamar yadda ake dafa shi abinbcin,wuraren da ake Kashi, da Wanka ba kasafai bane ake kulawa da tsaftace su ba.
Bugu da kari rashin nome ciyawa ko barin ruwa yana tsayawa ba tare da wucewa ba, kamar kwata inda ruwa maras kyau ke shiga ya taru, idan ba a kwashe shi lokaci- zuwa lokaci akwai yiyuwar sauro ya samu damar yin kwayaye wadanda idan suka kyankyashe yawansu zai karu wannan ma wata matsala ce.
Hanya ce da zasu yadu su samu damar yada cutar zazzabin cizon sauro.