Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Cheslea, Mauricio Pochettino, ya yi kira ga magoya bayan Chelsea kan halin da kungiyar ke ciki na kasa taka rawar da ta dace a bana.
Chelsea ta yi rashin nasara ranar Asabar din da ta gabata a filin wasa na Stamford Bridge da ci 2-0 a hannun Brentford, hakan ya kai kungiyar mataki na 11 a kan teburin gasar Ingila.
- Jiragin Sama Ya Yi Hatsari Dauke Da Ministan Tinubu Na Wutar Lantarki A Ibadan
- Kotun Daukaka Kara Za Ta Fara Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano A Ranar Litinin
Magoya bayan kungiyar sun yi wa ‘yan wasan Chelsea a lokacin da suke fita daga fili ihu, bayan tashi wasa da Brentford, karo na uku da aka doke ta a Stamford Bridge a bana. Tuni tsohon kociyan Tottenham da Paris St Germain ya fara fuskantar kalubale, bayan da Chelsea ta kasa komawa kan ganiya duk da fitattun ‘yan wasan da ta saya da tsada a bana.
Kociyan ya ce tuni suna sane da bacin ran da ke tare da magoya bayan Chelsea, amma dai akwai wasu abubuwan da suka sa kungiyar take wannan halin kuma nan gaba kadan komai zai wuce. Pochettino ya kara da cewar idan Chelsea ta dauki Carabao Cup na bana,
zai dan faranta ran magoya bayan kungiyar, sannan ya kara da cewar zai mayar da hankali sosai wajen yadda zai dauki Carabao Cup da FA Cup a kakar nan, hakan zai saukaka aikinsa a kungiyar.