Tsohon dan wasan Chelsea Eden Hazard wanda ya bayyana ritayarsa daga harkar kwallon kafa ya bayyana cewar yana da burin wata rana zai dawo Chelsea a matsayin mai horarwa.
Ya lashe kofunan Premier biyu a lokacin da yake Stamford Bridge.
- Arsenal Ta Nuna Sha’awar Daukar Osimhen Idan Ya Yanke Shawarar Barin Napoli
- Me Yake Faruwa Da Kungiyar Brighton A Kakar Bana?
“Bayan shekaru 16 tare da buga wasanni sama da 700, ya yanke shawarar kawo karshen sana’ata a matsayin kwararren dan kwallon kafa,” in ji Hazar yayin bayyana ritayarsa.
Tuni Hazard ya yi ritaya daga buga wa kasar Belgium kwallo bayan ya kasance cikin tawagar da aka fitar da su daga gasar cin kofin duniya ta 2022 a lokacin wasan rukuni.
A Real Madrid, Hazard ya lashe kofin zakarun Turai, Kofin Duniya na Club World Cup, Super Cup na Turai, kofunan La Liga biyu, Copa del Rey daya da kuma Spanish Super Cup biyu.
Sai dai ana kallon zamansa a Spain a matsayin kasawa bayan ya zura kwallaye 7 kacal a wasanni 76 da ya buga a dukkan gasa.
Hazard ya fara taka leda a kungiyar Lille ta kasar Faransa inda ya zura kwallaye 50 a wasanni 149 da ya buga kuma ya taimaka wa kungiyar ta lashe kofin Ligue 1 da kuma Coupe de France a 2010-11.
Ya koma Chelsea ne a shekarar 2012, inda aka saye shi kan kudi fam miliyan 32 a tsawon shekarun da ya yi a Chelsea Hazard ya lashe kyautar Gwarzon ‘yan wasan PFA a 2014-15.
Hazard ya zura kwallaye 110 a wasanni 352 da ya buga a Blues, ciki har da wanda ya yi nasara a wasan karshe na gasar cin kofin Turai ta 2019 da Arsenal a wasansa na karshe a kungiyar.
A tsawon shekarun da Hazard ya shafe yana taka leda a kungiyoyin Turai ba sau daya ya ya lashe kofuna da dama da suka hada da Uefa Champions League, UEFA Europa League Premier League da sauransu.