• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ina Da Isassun Kuɗi, Ban Ciwo Bashin Ko Kwabo Ɗaya Don Gyara Jihar Zamfara Ba – Gwamna Lawal

by Sulaiman
4 months ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta karbi lamuni ko rance domin gudanar da ayyukan kawo sauyi da ake yi a duk faɗin jihar ba, kuma duk da haka yana da isassun kuɗi a ausun jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da ya yi da wasu Editoci a ofishin sa da ke Gusau, babban birnin jihar a ranar Laraba, inda ya yi cikakken bayani kan nasarorin da gwamnatin sa ta samu tun hawan sa mulki kusan shekaru biyu da suka gabata.

  • Me Ya Sa Kamfanonin Kasa Da Kasa Ke Da Imanin Gudanar Da Harkokinsu A Kasar Sin?
  • Hajji 2025: Kashi Na Farko Na Alhazan Abuja Sun Dawo Gida Nijeriya

Gwamna Lawal ya bayyana manyan ci gaban da aka samu a bangarori masu muhimmanci da suka haɗa da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, da ƙarfafa tattalin arziki.

LABARAI MASU NASABA

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu.

Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023.

A cewar sa, inganta haɗin gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara.

Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waɗanda aka kammala a ƙarƙashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haɗa da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya a dukkanin ƙananan hukumomi goma sha huɗu na jihar.

Gwamna Lawal ya kuma bayyana shirin gwamnatin sa na bunƙasa fannin haƙar ma’adanai, inda ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin fanni na bunƙasar tattalin arziki da ake samu a yanzu da aka samu daidaiton tsaro a jihar.

Da yake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da gaskiya da riƙon amana da kuma tafiyar ci gaban al’umma, Gwamna Lawal ya nanata cewa duk nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu an cimmasu ne ba tare da karbar rancen ko kobo ɗaya ba.

Ya kuma tabbatar wa da al’ummar jihar Zamfara cewa akwai wasu ayyukan ci gaba a nan gaba, domin gwamnatin sa ta ci gaba da mayar da hankali wajen ganin an samar da ci gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar al’umma a faɗin jihar.

Da ya ke amsa tambaya dangane da rikicin PDP, Gwamna Lawal ya yi imanin cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya wuce ɗan takarar ta na shugaban ƙasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, kuma ya samo asali ne daga faɗan son rai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

“Kowa yana da nasa batun; ba wai batun Atiku Abubakar ba ne, ya wuce shi,” inji shi.

“Matsala ce ta cikin gida a cikin PDP, kuma muna yin ƙoƙari sosai. Ina ganin abin ya shafi kishin mutane ne, kowa da kowa.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Asuu
Labarai

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

October 14, 2025
Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato
Manyan Labarai

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa
Labarai

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Next Post
Yanzu-yanzu: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jami’ar Neja Bayan Kashe Ɗalibi

Yanzu-yanzu: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jami'ar Neja Bayan Kashe Ɗalibi

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

October 14, 2025
Asuu

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

October 14, 2025
Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

October 14, 2025
Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

October 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.