Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusif Gawuna, ya bayyana cewa ya tattara kwarewar da ake bukata domin mulkar Jihar Kano.
Kamar yadda daraktan yada labaran mataimakin gwamnan Hassan Musa Fagge, ya shaidawa LEADERSHIP hausa.
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Kashe Mutum 1, Sun Kwato AK47 A Kebbi
- Amurka Mai Satar Mai Daga Kasar Sham
Gawuna, ya bayyana haka ne cikin wani shirin talbijin na siyasa mai taken “Matsayar Siyasa A Yau” inda ya ce kasancewarsa wanda ya yi aiki da gwamnatoci uku, kuma ya zama shugaban karamar hukuma har karo biyu, kwamishinan ma’aikatar gona karo uku yanzu kuma yake matsayin mataimakin gwamnan Jihar Kano, wannan ya ba shi nagarta sama da sauran ‘yan takarkarun.
“Jama’ar Kano su ne za su yi alkalanci kasancewar sun san wane dan takara ne ke da nagarta da dacewar mulkarsu, saboda haka da gudunmawarsu da goyon bayansu zamu lashe zabe da yardar Allah.
“Gwamnatinmu mai ci a halin yanzu, ta gudanar da manyan ayyuka kuma masu nagarta tare da sauran tsare-tsare a kokarin ciyar da Jihar Kano gaba.”
Gawuna ya ci gaba da cewa, rarrabuwar kawuna a cikin sauran jam’iyyu nasara ce a gare mu. Mu ‘yan jam’iyyar APC kanmu a hade yake.
“Wadanda ke ta tururuwar shigowa cikin jam’iyyarmu, mutane da suka aminta da tsare-tsaren jam’iyyar APC domin mun zabi nagartattun ‘yan takarkaru. Wadanda zasu ba da gagarumar gudunmawar samun nasarar zabe, amma wadanda ke komawa wasu jam’iyyun na yin haka ne kawai domin bukatar yin takara sakamakon fadjwarsu a zaben fidda-gwani,” In ji shi.
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tsayar da Nasiru Yusif Gawuna da Murtala Sule Garo, a matsayin wadanda zasu yi wa APC takarar gwamna da mataimaki a jihar.