• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

by Rabi'at Sidi Bala
3 hours ago
in Nishadi
0
Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafi ne da ya saba zaƙulo muku fitattun jarumai, manya da ƙanana har ma da mawaƙa, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wani baƙon na musamman. Jarumi kuma mawaƙi, kana Malami mahaddacin Alƙur’ani mai gabatar da Tafsiri, wato UMAR HASSAN SAHIBUL ƘUR’AN Wanda aka fi sani da MAI FARIN JINI/GWANI UMAR. Inda ya warwarewa masu karatu zare da abawa game da abin da ya shafi harkar fim ɗinsa, da irin ƙalubalen rayuwar da ya fuskanta ta dalilin shigarsa masana’antar Kannywood, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko za ka faɗawa masu karatu cikakken sunanka, tare da sunan da aka fi saninka da shi.

Sunana Umar Hassan SAHIBUL ƘUR’AN, wasu kuma sun fi sanina da Mai Farin Jini, wasu kuma Gwani Umar.

Me ya sa ake kiranka da mai farin jini?

Abun ya samo nasaba ne daga gida, ɓangaren mahaifiyar mu ta ce, tunda take haihuwar yaro ba a taɓa yaron da mutane suka zo da rububin sunansa ba iri na. Sannan lokacin da nake ƙarami kowa na son ɗauka ta a fita da ni. Watarana kuma wani malami yana son kiran sunana bai san sunana ba, sai ya laƙana min Umar Mai farin jini. A haka dai sunan ya riƙa zagawa har ya bi ni.

Labarai Masu Nasaba

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

  • Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
  • Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN

Ko za ka faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinka?

Ni haifaffen ɗan Zaria ne, wani gari da ake cewa, Samaru ana yi masa laƙabi da Samarun Zaria. Kuma nan nake a Hayin Dogo layin Ɗahiru Baban Naira. A nan na tashi tare da iyayena, mahaifina ana ce masa Malam Hassan mai maganin gargajiya, gida mai almajirai. Bayan na taso iyayena suka kai ni makarantar Allo, bayan nayi shekaru biyu aka dawo da ni aka saka ni a firamare. Na samu na yi ‘primary three’ dan ko gamawa ban yi ba, daga nan aka ƙara kai ni karatu. Haka dai na yi ta yawo irin su; Katsina, Kaduna, maraban Jos, Ƙauyen Gwauro, dan a can ruwa ya kusa haɗiye ni, saboda na yi kamun kifi a can. Bayan nan aka je har su Sokoto, Birnin Kebbi, Nijer, Kano zuwa yanzu ina zaune a garin Kaduna, cikin horewa ta Allah ya ba ni iko na haddace alƙur’ani. Sannan kuma na rubuta alƙur’ani a yawon da nake yi, a yanzu kuma ina matakin malamin Tafsirin Alƙur’ani.

Ka yi maganar cewa ruwa ya kusa haɗiye ka, shin me ya janyo hakan, kuma ya abun ya kasance?

Lokacin da na je makarantar Allo muna zuwa mu yi ice mu zo mu siyar, domin mu samu kuɗin omo da na kashewa. Dajin da muke yo icen ya zamo akwai birrai a ciki, abu na biyu sai an tsallaka ruwa sannan muke zuwa dajin mi yo icen. Wata rana mun je mun dawo muka tarar da kwale-kwalen da yake ɗaukar mu, gabaɗaya ranar ba mu tarar da kwale-kwale koɗaya ba. Daga ƙarshe waɗanda suka iya ruwa suka yi iyo suka tsallaka ruwan, wasu kuma suka ɗan hau galan, wasu kuma suka hau kwarya. To, ni kuma ban iya ba, kawai sai na hau kan itacen nan irin ni ma ya tsallako da ni to, daga nan ne ruwan ya kife da ni Allah ya taƙaita ban mutu ba aka zo aka tsamo ni.

Da yawan mutane za su yi mamakin ganin yadda ka ke malami mahaddacin alƙur’ani, kuma ka tsunduma harkar fim, me za ka ce akan hakan?

Eh, gaskiya mutane suna wannan mamakin sosai. Wasu sukan ce asiri ne, wasu kuma sukan ce ai hau ne ma ya faɗa min, in ban da haka babu yadda za a ce mahaddacin alƙur’ani kuma marubucin alƙur’ani, ya zamana yana wannan harkar. A ‘yan fim ɗin ma akwai jarumai da yawa da sun sha faɗa min kaf! ‘yan fim babu kamata. Akwai masu ilimin addini sosai amma wanda za a ce ya haddace alƙur’ani har ya rubuta shi kaf ‘yan fim babu kamata. Wasu daga cikin mutane waɗanda ba su zauna da ni ba suna ganin kamar ma ni ba musulmin kirki bane, irin ana ɗan kyama ta, ana kyara ta sosai. Ina fuskantar baƙaƙen maganganu, dan ko kwanan nan wani ya kafa hoto na ya zaga da makamancin haka. Amma duk masu zagin idan mun zauna haka sai suka fuskance ni, kuma duk wanda ya zauna da ni a gaske ya san na fi baiwa karatu mahimmanci fiye da waɗannan harkokin, sai kuma a ga waccen kyamar ta ragu. Har yanzu dai akwai mutanen da ba su fahimce ni ba, kuma mutane da yawa sun tsane ni, sun guje ni a kan hakan. Dan har wata yarinya na taɓa so wanda a raina ina jin ina so na aure ta, amma sakamakon wannan rigar ta fim ɗin yarinyar ta nuna ba ta yi. Kamar yadda mahaifinta ya nunan cewa, da zarar ina wannan harkar fim ɗin ba za su ba ni ita ba.

Lokacin da ake faɗar munanan kalamai a kanka game da fim, shin baka ji a zuciyarka kana son barin harkar fim ba?

Nii yadda na tashi inada dakakkiyar zuciya, saboda ina da kyakkyawar manufa ina da yaƙinin ni dai fim bai sa ni na yi shaye-shaye ba, kuma bai sa ni nayi hulɗar mata ba, bai sa ni na sauka daga kan asalin tarbiyyata ba. Saboda haka tunda ni na san tsakanina ga Allah na iya aktin ne kawai, kuma rayuwata ce ta gaske nake yinta, ban taɓa cewa zan bari ba. Lokacin da na ce zan bar fim shi ne lokacin da yarinyar da zan aura ta nuna bata so, sai na yanke hukuncin zan bar fim. A ranar ‘yan jarida sun gayyace ni za su yi hira da ni a kan hakan, wani fim an gayyacen na ce na daina, me ya jaho hakan?. Sai mahaifiyata ta kira ni take cewa “me ya sa za ka bar fim”, na faɗa mata yadda muka yi. Take ce min bata yarda ba, na tambaye ta me ya sa? ta ce ai duk abin da zan daina ta fi son in bari lillahi billahi ne, ba ta son saboda mace ya zamana na daina. Mun yi wannan ma ba da daɗewa ba sai ga kiran Lawan Ahmad da Ali Nuhu da sauransu kan wani sabon aiki da za mu fitar.

Za ka yi kamar shekara nawa da fara fim?

Zan yi kamar shekara uku da fara fim, amma na fara waƙa kusan shekara takwas kenan, duk da cewa na fi yin aktin yanzu, amma am fi sanina a fim.

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Gaskiya babu wani abu da zan ce ya ja hankali na, kawai dai tun ina yaro irin yadda in za a aiki yaro an san ba zai dawo da wuri ba, sai ace “Idan ka dawo da wuri zan kunna maka kallo ko zan saka maka waƙa” to, da haka ake yi min wayo sai na yi sauri na dawo. Idan na dawo sai a yi min hakan kuma ina jin daɗi tun ina ƙarami ban ma san mene fim da waƙa ba, amma na taso da mafarkin hakan. Kuma daman duk me son fim da waƙa zan iya cewa, wannan cuta ce kamar ta me soyayya. Wanda yake soyayya in bai sami cikon muradinsa ba, to, ba zai samu nutsuwa a soyayya ba to, haka ma fim da waƙa.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?

Na tashi ina ta budin-budimina, duk inda ake yahon dj, yahon kaɗe-kaɗe, garkuwa lokacin ana yahon Ajo da sauransu dai ina wajen. To, Allah dai bai sa da ni da wani mawaƙi ko ɗan fim ba, saboda ban tashi a garinsu ba. Wataran na je Katsina ina makaranta na fara biye-biyensu a ‘studio’, a nan na fara Ido. Bayan na yi ido a nan sai Allah ya sa na dawo Kaduna da zama, lokacin an ɗauke ni koyarwa a Kaduna. A nan ne na fara haɗuwa da ‘yan fim da mawaƙa, na fara alaƙa da su nake ganin yadda harkar take. Daga nan na ga ina da sha’awa. Bayan na fara tafiya ta yi tafiya har malamaina waɗanda suka kai ni makarantar dan na karantar suka ankara na fara ƙarfi a harkar aka ce an kore ni gabaɗaya makaranta. Nan dai na daina karantarwar na dawo a ƙarshe na koma makaranta na cigaba da karatuna. Inda na je ina haddato alƙur’ani na samu ɗan abin da na samu na ilimin alƙur’ani, sai na dawo. Sai kuma Allah ya kai ni Kano, daman Kano inada furodusas da daraktos da ake mutunci da su, sai na sauka a gidan ɗan fim kuma furodusa wato Muddasir Isyaku Dutsenma. Duk inda zai je harkar fim da ni yake tafiya, daman a Kaduna na fara da waƙa, daga baya ne na juye na koma fim.

Ya batun iyaye lokacin da za ka sanar musu kana son shiga harkar fim, shin ka fuskanci wani ƙalubale daga gare su ko kuwa?

Eh! Na fuskanci ƙalubale me yawa, saboda ni gidan da na tashi gidan almajirai ne. Ba a ma san mene waƙa ba, dan gidan mu ba TV har yau maganar da nake yi yanzu ba a san mene TV ba. Babbanmu ba ya riƙe babbar waya har yanzu, haka mahaifiyar mu to, ba su san mene kallo ba. Saboda haka ni na fuskance su na faɗa musu zan fara waƙa ko fim gaskiya wani abu ne me rauni gare ni, na dai fara ba su sani ba, da suka sani kuma a taƙaice an taɓa kora na daga gida saboda wannan harkar. An nuna min ɓacin rai sosai, sun nuna babu ruwansu da ni a gida, kuma a hakan na cigaba da yi. Saboda ni na san ina da kyakkyawan manufa, dan da na fara yi ɗin sai na gane akwai rawar da zan iya takawa ta iya fannin waƙa ko fannin fim. Amma inada zuciya mai kyau tunda na sami cikakken tarbiyya. Bayan lokacin korar da aka yi min a gida, iyaye suka kira suka ce, ‘To, tunda dai mun fahimci abun nan bai ɓata maka tarbiyya ba, baka lalace ba, ba ka daina karatu ba, in za ka yi fim ko waƙa ace ɗan mu ya tashi a mawaƙi gara ya zama jarumi irin yadda su Malam Inuwa suke yi ko Kabiru na Kango, tunda kana da ilimin addini ka zamo me bayar da gudun mawa ta wannan fannin. Sai na ga tunda iyaye su suka bayar da wannan shawarar sai na cigaba da tafiyar a haka. Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah.

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: FimHausa FimKannywoo
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Kammala Baje Kolin Hada-Hadar Cinikayyar Hidimomi Na Sin Na Shekarar 2025

Next Post

Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

Related

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango
Nishadi

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

1 day ago
Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)
Nishadi

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

1 week ago
Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
Nishadi

Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

2 weeks ago
Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah
Nishadi

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

3 weeks ago
Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
Nishadi

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

4 weeks ago
Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu
Nishadi

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

1 month ago
Next Post
Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

LABARAI MASU NASABA

Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

September 14, 2025
Kasar Sin Na Samarwa Duniya Damammaki A Fannin Hada-hadar Ba Da Hidima

Kasar Sin Na Samarwa Duniya Damammaki A Fannin Hada-hadar Ba Da Hidima

September 14, 2025
Duba Ga Kwaɗayi Da Son Duniya A Tsakanin Matan Wannan Zamanin

Duba Ga Kwaɗayi Da Son Duniya A Tsakanin Matan Wannan Zamanin

September 14, 2025
Jagororin Kamfanonin Ketare Sun Nuna Gamsuwa Dangane Da Zuba Jari A Kasar Sin

Jagororin Kamfanonin Ketare Sun Nuna Gamsuwa Dangane Da Zuba Jari A Kasar Sin

September 14, 2025
Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

September 14, 2025
Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

September 14, 2025
An Kammala Baje Kolin Hada-Hadar Cinikayyar Hidimomi Na Sin Na Shekarar 2025

An Kammala Baje Kolin Hada-Hadar Cinikayyar Hidimomi Na Sin Na Shekarar 2025

September 14, 2025
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

September 14, 2025
Shugabanci A Nijeriya: A Ina Ne Gizo Ke Saƙar?

Shugabanci A Nijeriya: A Ina Ne Gizo Ke Saƙar?

September 14, 2025
Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

September 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.