Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta kasar Argentina da Inter Miami, Lionel Messi, ya bayar da sharadin da zai sa ya buga wa Argentina wasa a gasar FIFA World Cup na shekarar 2026 da za a buga a kasashen Arewacin Amurka, za a buga gasar cin kofin Duniya na 2026 a manyan biranen kasar Kanada, Amurka da Medico a lokacin bazara, kuma ana sa ran gwarzon dan wasan na Argentina zai halarci gasar.
Duk da haka, Messi ya ce zai shiga tawagar Argentina ne kawai idan yana cikin koshin lafiya, yana mai tabbatar da cewa ba ya son zama nauyi ga tawagar, Messi ya jagoranci Argentina zuwa ga nasara a gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 inda suka doke Faransa a wasan karshe, Messi zai zama daya daga cikin ‘yan wasa biyu kacal da za su buga gasar cin kofin Duniya har sau shida, tare da Cristiano Ronaldo.
- Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani
- BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani
A wata hira da Sport, an tambayi dan wasan mai shekaru 38 game da buga wasa a Gasar Cin Kofin Duniya na FIFA mai zuwa ta 2026, tauraron dan wasan Argentina ya ce, “Eh, a bayyane yake, Gasar Cin Kofin Duniya, wasa ne na musamman ga tawagar kasa, akwai bukatar a saka naci wajen ganin an samu nasara,” in ji Messi.














